Da ɗumi-ɗumi: Ɗaya daga cikin malaman da suka yi muƙabala da Sheikh Abduljabbar Kabara ya rasu

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Guda daga cikin malaman da suka yi muƙabala da Malam Abduljabbar Kabara, Malam Mas’ud Mas’ud Hotoro ya rasu.

Rahotanni da MANHAJA ta samu sun nuna cewa Malam Mas’ud ya rasu ne a daren ranar Larabar da ta gabata sakamakon haɗarin mota da ya auku a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya

Idan za a iya tunawa dai malamin na ɗaya daga cikin mutum huɗun da suka yi muƙabala da Sheikh Abduljabbar Kabara a kwanakin baya.

Kazalika, Malamin shi ne wanda ya wakilci ɓangaren Ƙadiriyya yayin zaman muƙabalar.

Rahotannin sun bayyana cewa an yi wa Malamin jana’aiza a yau Alhamis a gidansa da ke Hotoro da misalin ƙarfe 2:00 na rana.