Marubuta mutane ne masu wuyar sha’ani – Zaharadden Kallah

“Dole marubuci ya zama makaranci”

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Idan ana maganar rubutu da ƙungiyoyin marubuta, musamman shahararriyar ƙungiyar nan ta marubutan Nijeriya, wato ‘Association of Nigerian Authors’ (ANA), to tabbas za a sa sunan baƙonmu na yau. Wannan ba kowa ba ne sai Zaharadden Ibrahim Kallah, domin kuwa ya shekara 25 a harkar rubutu, jajirtacce ne kuma mai matuqar ƙwazo, wanda da ƙoƙarinsa ne ƙungiyar ANA reshen Jihar Kano ta kafu. Wakilin Manhaja a Kano, Ibrahim Hamisu, ya zanta da shi. Don haka ku biyu mu don jin yadda hirar za ta kasance:

Manhaja: Za mu so jin taƙaitaccen tarihinka?
ZAHARADDEEN IBRAHIM: Suna na Zaharaddeen Ibrahim Kallah. An haife ni a unguwar Fagge da ke Kano. Na fara karatu a makarantar firamare ta Giginyu, daga baya na koma firamare ta ‘Race Course’ da ke filin Sukuwa. Na yi makarantar Islamiyya ta Madrasatul Deen Wattahzeeb, Giginyu. Na je makarantar sakandire ta Stadium inda na kammala a shekarar 1995. Na yi makarantar share fagen shiga Jami’a ta CAS Kano, inda daga nan na shiga jami’ar Bayero Kano, na karanci fannin zamantakewar al’umma da siyasa (Sociology/Political Science). Na yi digirina na biyu a fannin cigaba (Development Studies), a jami’ar Bayero, Kano. Ina aiki da jami’ar Bayero, Kano a ɓangaren ‘Registry’. Na riƙe muƙamai a ƙungiyar Marubuta Ta Nijeriya (ANA), har na yi shugabancinta karo biyu. Sannan na taɓa riƙe Ma’aji na ‘Northern Nigeria Writer Summit’ a matakin ƙasa.

Ta yaya ka samu kanka a harkar rubutu?
Na fara samun sha’awar rubutu ne tun daga makarantar firamare, inda muke karanta littattafai irin su ‘Baba da Inna’ da ‘Ilya Ɗan Maiƙarfi’ da ‘Ruwan Bagaja’ da ‘Magana Jari Ce’ da ‘Zaman Mutum Da Sana’arsa’ da sauransu. Ban samu kaina a cikin rubutu ba sosai sai a lokacin da na shiga makarantar sakandire. A lokacin ne na fara ƙoƙarin rubuta gajerun labarai. Sannan a wannan lokaci ne Farfesa Yusuf M. Adamu ya ƙarfafe ni. Duk sanda ya yi sabon littafi zai ba ni na karanta tare da jin ra’ayina. A 1996 Farfesa Yusuf ya fara gayyata ta taron ANA Kano a gidan Ɗan Hausa, wanda aka shirya don shagalin bikin sallah. A lokacin na fara ganin Salihu Alkanawy da Ado Ahmad Gidan Dabino da Hajiya Balaraba Ramat Yakubu da Ahmad M. Zaharaddeen da sauransu. Tun daga wannan lokaci sai na shiga rubutu sosai. 

Me ya ja hankalinka ka shiga harkar rubutun?
Harkar rubutu makaranta ce mai zaman kanta, domin idan har za ka yi rubutu mai ma’ana sai ka kasance makaranci. Na kasance ma’abocin karance-karance musamman na Hausa, kusan littattafan Hausa na wannan lokaci na karanta su. Wannan ya sa min sha’awa ni ma na fara rubutu domin al’umma su amfana da na wa rubutun. 

Littafai nawa ka rubuta daga lokacin da ka fara rubutu zuwa yau?
Na jima ban fitar da littafi ba, domin a wancan lokaci idan ka yi rubutu yawanci ‘yan kasuwa ke bugawa, za a sa sunanka amma su ke cin moriyar. Don haka na gwammace na ta ajiyar ‘manuscripts’ ɗina har lokacin da zan samu halin bugawa. Na rubuta littattafan Hausa guda shida, amma guda biyu ne suka fita, ‘Sadauki Mai Duniya’ da ‘Ƙarkon Dabino’ da mu ka yi da Ɗan Azimi Baba Cheɗiyar ‘Yangurasa. Na rubuta littattafan Turanci guda biyu ‘The Right Choice’ da ‘After a Long Silence’. Ina cikin editoci na littafin gamayyar Turanci na gajerun labarai mai suna ‘Telling Our Stories’. Na rubuta gajerun labarai da waƙoƙi na Hausa da suka fito a littattafan gamayya da suka haɗa da: ‘Five Hundred Nigerian Poets’ da ‘Mazan Fara’ da ‘Crumbled Spell’ da ‘Ƙwaryar Ƙira’ da ‘Voices from the Savannah Poets’ da ‘Capital: A Poetry Anthology’ da ‘War on Corruption and Other Poems’. Bayan waxannan, rubuce-rubucena da dama sun fito a mujallu da jaridu a gida da waje. 

Ka na cikin shugabannin ANA ta Kano da suka daɗe suna jagorantar ƙungiyar. Waɗanne irin nasarori ka samu a lokacinka?
Haka, zan iya cewa ni ne na fi kowa jimawa a cikin shugabancin ANA Kano, domin na fara ne tun daga Auditor I a shekarar 2000. Na sauka daga shugabancin ANA a 2021, amma a yadda kundin tsarin mulkin ƙungiyar ya ke sai na sake yin shekara biyu a matsayin ‘ex-officio’ domin ba da shawarwari ga waɗanda suka gaje mu. Idan Allah ya kai mu 2023 na ke sa ran yin ritaya don in huta. Da fatan za ku fito min da fansho da giratuti a kan lokaci. (Dariya). To, alhamdu lillah, an samu nasarori da dama. Ka san marubuta mutane ne masu wuyar sha’ani, saboda yadda suke kallon duniya da abubuwa da dama. An samu rashin fahimta tsakanin marubuta a baya, wanda mun yi ƙoƙarin ganin an dawo an haɗe, domin samun ɗorarren cigaba. Da yawansu suna ganin tun da na hau shugabanci, dole su zubar da makamansu. A nan dole na yi godiya ga irin haɗin kan da aka bani daga manyan yayye da ƙannena a rubutu, har da iyaye. Bayan wannan mun yi ƙoƙarin shigo da ayyuka da za su jawo matasa, domin su ne za su maye gurbin tsofaffin marubuta. Misali, ANA Kano da haɗin gwiwar CITAD mun shirya horon sanin makamar aiki a kan rubutu ga makarantun sakandire 15 a Kano. Bayan horon, mun dinga zagayawa makarantun domin halartar karatu na musamman da suke shiryawa. Mun shirya ‘Makon Adabi Na Kano’ (Kano Literary Week) sau uku, waɗanda a cikinsu an gabatar da ayyuka da dama da suka ƙunshi horarwa a kan rubutu, gasar kacici-kacici ga ɗalibai, tattaunawar marubuta, karatu na musamman da bajakolin littattafai. Sannan akwai abin da mu ka kira ‘reading through role models’, inda manya a gari kan fito su karanta littafi ga yara don ƙarfafar ɗabi’ar karance-karance. Manyan da suka amsa wannan gayyata akwai Sarkin Kano na 14, Mai Martaba Muhammadu Sanusi II da Alhaji Bashir Othman Tofa da Sheikh Ibrahim Khalil da Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, da Umar Muhammad Jigirya da Dakta Mannir Suleiman da Farfesa Abdulrazak Garba Habib, da Ibrahim Mandawari da Sa’adatu Baba Ahmad da Lawan Adamu Giginyu da Safiya Ibrahim Abdulhamid da marubuta da dama. Duk an zaƙulo su ne daga fanni daban-daban da suka ƙunshi masu mulki, da malamai da likitoci da marubuta da ‘yan fim da sauransu. Bayan wannan an ƙarfafi dandalin marubuta da ake gudanarwa a ɓangaren Hausa da Turanci a duk wata tare da gabatar tsarin baƙon marubuci, inda akan tattauna da marubuta. Sannan mun yi ƙoƙarin ƙarfafa alaƙar qungiya da wasu hukumomi da manyan makarantu da suke da ruwa da tsaki a harkar rubutu. Da yawansu mun yi ayyukan cigaban ilimi da rubutu tare. 

Ta ɓangaren ka, waɗanne nasarori ka samu a harkar rubutu?
Alhamdu lillah, suna da yawa. Da farko akwai ƙulluwar alaƙa da marubuta da dama a faɗin ƙasa da wasu sassa a duniya. Na biyu, na halarci manyan tarurruka da suka jiɓanci rubuta da marubuta a gida da Ƙasar Nijar. Sannan an buga ni a manyan ƙasidu da littattafai na zahiri da na yanar gizo.

Ƙalubale fa; akwai ko babu?
Tun a farkon fara rubutuna, matsalar farko da na fuskanta ita ce ta kuɗi. Domin a zamanin da mu ka fara rubutu zuwa yanzu, abu ne mai wuya a samu masu ɗab’i (publishers) da za su buga rubutun sabon marubuci a tsarin buga littafi da aka sani a duniya, wanda kamfani zai buga littafin marubuci babu kwabonsa, sannan a dinga bashi kasafinsa daga ribar da aka samu. Dole marubuci ya buga littafi a tsarin buga littafi na kai tsaye, wanda yana buƙatar kuɗi idan har yana son ganin littafinsa. Matsala ta biyu ita ce rashin tabbataccen tsarin kasuwanci da yaɗa littattafai. Kowanne marubuci yana buqatar rubutunsa ya shiga loko da saƙo. Amma abin zai yi wuya a ce kai ne marubuci, kai ne mai bugawa sannan kai za ka yi kasuwancinsa da yaɗa shi.

Yawaitar marubutan ‘online’ a wannan lokaci cigaba ne ko ci-baya?
Cigaba ne, domin zamani ne ya kawo shi. Yanzu muna ƙarni na 21, wanda ƙarni ne da ya kawo na’ura mai ƙwaƙwalwa da sadarwar yanar gizo wato ‘internet’. Yanzu a duniya a kafofin sadarwar yanar gizo ce hanyar haɗa ilimi da rubutu a duniya. 

Me ka ke ganin ya sa harkar rubutun littafi ta ja baya ta yadda wasu marubutan suka koma fim?
Harkar fim wani sashe ne mai zaman kansa, kuma dama wasu sun fara rubutu a baya ne saboda harkar fim ba ta kafu ba. Da harkar fim ta zo, sai suka koma abin da tuntuni suke da sha’awa a kai, ba wai saboda harkar rubutun ta lalace ba. Ita kuma harkar rubutu ta gamu da sauyin zamani ne, yawancin makaranta yanzu suna kan ‘social media’. Kuma dama ka san tun da manyan kamfanoni suka daina buga littattafan marubuta aka koma bugawa da kai (Self Publication), hakan ya sa an dinga samun naƙasu a ɓangaren ingancin rubutu da na ɗab’i. Wannan ya taimaka wajen karkata ko raguwar makaranta. Bayan wannan kasuwancin littafi ya koma tsarin saye da sayarwa na yanar gizo, wanda har yanzu marubutan Hausa ba su rungume shi yadda ya kamata ba. Domin akwai tarayyar kasuwanci da wasu littattafan, wanda dole a inganta aiki idan ana son a yi nasara a kasuwar zamani.

A wane lokaci ka fi jin daɗin rubutu?
Ina yin rubutu a kowanne lokaci idan rubutun ya zo. Amma idan ina yin dogon aiki, na fi yin sa da daddare ko da sanyin safiya.

Ka taɓa samun lambar yabo a rubutu?
Eh, na samu lambobin yabo da kambuna a rubutu da suka ƙunshi:

  1. A shekarar 1997, ‘Manuscript’ ɗina ‘Lokaci Baƙo Ne’ ya zamo zakara a gasar rubutu ta Nijeriya da kamfanin ɗab’i na Mazari suka sanya. A shekara 2004 na zamo zakara a gasar rubutun waƙen Turanci ta duniya da wata hukuma a Belgium da haɗin gwiwar Nijeriya ta shirya. A shekara 2010 na ɗauki mataki na uku a gasar waƙen Turanci da hukumar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa da cin hanci ta Jihar Kano ta shirya. A shekara 2019, ‘Manuscript’ ‘Marucin Kan Dutse’ ya zamo na biyu a gasar rubutu ta Aliyu Mohammed Reserach Library. A shekarar 2018, gajeren labari na mai taken ‘Fate Has Been Sealed’ ya lashe gasar ‘BUK Creative Writers Forum’ na wata-wata da Farfesa Mustapha Muhammad ya sanya. Na karɓi lambobin yabo da dama daga ɓangarorin adabi, ilimi, cigaban al’umma da sauransu.

Da wa ka ke koyi a harkar rubutu?
Ina koyi da rubutun Sidney Sheldon a Turance. A Hausa ina koyi da Abubakar Imam. Sannan rubutun Bala Anas Babinlata ya yi tasiri sosai a rubutuna. 

Wane kira za ka yi ga marubuta masu tasowa don ƙara inganta rubutu?
Da farko sai sun jajirce tare da ƙaunar abin da suke yi, ta yadda ba neman kuɗi ko suna ba ne jigon abin da ya kawo su rubutu. Idan akwai sha’awar harkar, za su jure duk wani ƙalubalen da ke cikinta. Wannan juriya za ta zamo mabuɗin duk wani buri da suke da shi a rubutu. Sannan dole su kasance masu ɗabi’ar karance-karance tare da karanta ayyukan manyan marubuta.

Madallah, mun gode.
Ni ma na gode.