Hanyoyin magance ciwon basur

Daga ABILKISU YUSUF ALI

Yadda ciwon basir ya ke da hanyoyi da yawan gaske da ke haifar da shi sannan yake da alamomi da ke nuna alamunsa haka kuma hanyoyin magance shi yake da yawan gaske. Akwai basir da ba ya buƙatar shan magani ana iya magance shi ne da ɗabi’a, wato yanayin rayuwa ta yau da kullum ko kuma abin da ake ci.

Sannan akwai basir da na lokaci ne in wannan yanayin ya wuce da dama ana samun waraka. Misali, mai ciki, Basir kan dami mai juna biyu wanda nauyin ɗa ne ke janyo shi, irin wannan basur ɗin da dama da mace ta haihu sai ya baje.

-Yana daga alamun basir yawan fitar da iska (tusa).

-Yawan zama wuri ɗaya yana haifar da basir, da mutum zai taƙaita zaman ko kuma yake tashi ya ɗan zagaya lokaci zuwa lokaci za a samu sauƙin kamuwa da shi.

-Yawan motsa jiki yana hana basir tasiri. Don masana sun ce masu ƙiba sun fi samun hatsarin kamuwa da basur.

-Taƙaita cin abinci mai tauri ba tare da shan ruwa ba ko wani sirki yana haifar da taurin bayan gida wanda wannan ke haifar da basir musamman mai fitar baya.

-Cin ‘ya’yan itatuwa musamman lemon zaƙi yana hana basir tasiri.

-Shan Habbatus sauda da aka cuɗe da zuma a sha cokali bibbiyu sau uku a rana da yardar Allah za a rabu da basir kowanne iri ne.

-Ga basir da yake fitar baya kuwa, ana samun garin hulba da garin bagaruwa ta ƙasa a tafasa shi in ya ɗan huce ba zafi wanda zai cutar ba ake shiga cikinsa har ya huce gaba ɗaya a yi haka kullum sau ɗaya za a dace da yardar Allah.

-Cin tafarnuwa da aka yanka ƙanana-ƙanana da tumatir yana warkar da basir na ciki.

-Ga mai ciki da take fama da basir ta dimanci kayan itatuwa musamman lemon tsami sannan ta rage shan abu mai zaƙi don yana haddasa basir musamman mai fitar baya.

-Yayin da ciwon basir ya yi tsanani yana da kyau a nemi shawarar ma’aikatan lafiya don a kimiyance ana yin aiki a cire shi.

-Yawan cin ganyayyaki a abinci ko ma a matsayin abincin.

-Yawan shan ruwa shi ma yana warkar da basur da na cikin da mai fitar baya.

Ga mai tambaya ko ƙarin bayani yana iya tuntuɓar wannan layin amma tes kawai ko ta whatsup 08039475191 ko a page ɗina na facebook Bilkisu Yusuf Ali