Gwmanatin Tarayya ta bayyana dakatar da shirinta na janye tallafin fetur har sai abin da Allah Ya yi.
Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsaren Ƙasa, Hajiya Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan yau a Abuja.
Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa kan sabbin kafofin yaɗa labarai, Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na facebook cewa, dakatar da shirin ya biyo bayan rashin goyon baya da Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna ne kan cire tallafin na fetur.
