WASIƘU: Zaɓin ’yan Nijeriya a 2023

*Iyaye a Arewa ku ji tsoron Allah kan sauke haƙƙin ’ya’yanku
*Kira ga matasa su guji faɗa wa cikin hatsarin sha’awa

Duk da cewa ba matsayi guda ne kaɗai ake zaɓe ba amma wanda aka fi magana a kai guda ne. Magajin kujerar shugabancin ƙasa. Amma kafin akwai ta gwamnonin jihohi da ta ’yan majalissun jihohi zuwa na tarayya don haka mu dubi hasashen makomar kujera ta ɗaya bayan zaɓen 2023. Tun a karon farko an ji wasu ’yan siyasa daga ɓangarorin kudanci sun bayyana muradin su.

Tsohon gwamnan Legas Chief Bola Ahmed Tinubu kuma jigo a Jam’iyya mai mulki APC ya shelanta kai na ne. Haka nan tsohon gwamnan Abia Orji Uzor Kalu ya fito ya bayyana kai na ne. Gwamnan Ebonyi David Nweze Umahi ya fito ya nuna muradinsa. Kar mu manta ita ma babbar jam’iyya mai adawa PDP da nasu mutanen haka sauran ƙananan jam’iyyu duk za a ji su a nan gaba.

Ni a tawa ’yar shawara ga dangi na talakawa musamman a arewa. Mu nutsu duk wanda zai fito ya fito amma cencenta ta zamo mizani bayan addu’a domin an ce tun za a ake shiri. Allah ya kai mu lokuttan lafiya. 

DagaMukhtar Ibrahim Saulawa.
07066434519/08080140820.

Iyaye a Arewa ku ji tsoron Allah kan sauke haƙƙin ’ya’yanku

Assalamu alaikum, Manhaja. Barkanku da aiki, muna muku fatan Allah ya ƙara muku ƙwazo, Ameen. Ina kuma muku addu’a Allah ya ƙara muku hikima da basirar aiki da kuma bunƙasa wannan jarida mai farin jini baki ɗaya.

A Arewa ne za ka samu gidan Almajirai da yara ba adadi, a Arewa ne za ka samu iyaye sun sake yaran su ana kwashewa ana sauya musu addini, a Arewa ne za ka samu gidan kangararru inda ake tara ɗaruruwan yara wai da sunan sun gagari iyayensu.

Kwanaki kaɗan da suka wuce wata baiwar Allah ta saka wani bidiyo a shafin sada zumunta na Tuwita, inda yara mata ƙanana waɗanda shekarunsu bai wuce 15 ba, suna neman a sanya musu alluran hana ɗaukar ciki. A cikin bidiyon da aka tambaye su ko me za su yi da shi alhalin ba su da aure? sai suka ce talla ne aikin su. Matuƙar suka dawo gida ba tare da ciniki mai yawa ba, to koran su za a yi a gida.

Har yanzu jami’an tsaro ba su gama kwato yara da ’yan kudu (Qabilar Ibo) suka wawushe daga Arewa ba. Waɗannan yara an ci zarafin da yawa daga cikin su kuma an keta musu haɗi. An tirsasa su bin addinin da ba su da alaƙa da shi.

Abin da zai ba ka mamaki shi ne, saboda tsabar rashin kula, iyayen waɗannan yara ba su nemi yaransu ba lokacin da suka ɓata. Ba su haɗu suka sami gwamnati a kan cewa ana kwashe musu yara ba tare da sun san su waye ba. Taimakon Allah ne kawai ya sa aka kama ɓarayin yaran. Idan da jami’an tsaronmu ba su kama su ba, to da shiru za ka ji.

Har ila yau, a Arewar mu ne aka bankaɗo gidajen kangararru. Irin waɗannan gidaje an yi su ne don karɓar yara daga hannun iyaye da sunan sun kangare. Jami’an tsaro sun gano cewa ana ketawa yara haɗi ta hanyar luwaɗi da su, hakazalika yaran na fama da cututtuka daban-daban.

Shin me ya sami iyaye ne a Arewa?
Ko iyaye sun manta cewa haihuwa kyauta ce daga Allah maɗaukakin sarki, wanda duk wanda aka ba shi to akwai haƙƙoƙi a kansa?

Ko iyaye sun manta cewa haƙƙin ciyar da yaransu, tarbiyyantar da su, tufatar da su, samar musu matsuguni da ba su ilimi duk ya rataya a wuyan su ne?

A kowani lokaci da iyaye suka yi wasa da haƙƙoƙin yaransu, to tamkar suna sake kuraye ne a cikin al’umma. Waɗannan yara za su nemi su ci koda kuwa ta wani hanya ne. Za su nemi su sanya tufafi ko ta wani hanya, za su nemi su ji daɗin rayuwa ko ta wani hanya.

Yaron da ya rasa samun haƙƙoƙinsa a wurin iyayensa to ya samu matsala. Ba zai iya fahimtar daidai da kuma ba daidai ba. Tunaninsa ya samu tasgaro, cikin lokaci ƙarami zai iya zama bala’i a cikin al’umma.

Daga Mustapha Musa Muhammad; ɗalibi a fannin karatun Injiniyancin Sinadarai (Chemical Engineering) a Jami’ar Federal Polytechnic Kaduna, 09123302968.

Kira ga matasa su guji faɗa wa cikin hatsarin sha’awa

Assalam alaikum. Babban abin da ke addabar matasa maza da mata shi ne, sha’awa. Kusan kullum matasa na faɗawa cikin bala’in fasiƙanci kala-kala a dalilin rashin sanin hanyar kaucewa haka. Idan mutum ya yi duba na tsanaki tare da la’akari da yanayinmu da kuma yanayin zamani da muke ciki zai ga cewar da yawa wasu na faɗawa cikin aikata fasiƙanci ba cikin son ransu ba, sai don abin ya fi ƙarfinsu.

Sau da yawa za ka ga matashi mai hankali mai tarbiyya mai tsoron Allah, ya san illar zina, ya san girman zunubinta, amma saboda fitinar sha’awa ya ka sa daurewa har sai ya je ya aikata ɗin. Wani haka zai ta aikatawa yana tuba da haka har zina ta zame masa jiki ya run ka ganin ai yinta ba komai ba ne.

Haka za ka ga yarinya kamila mai tarbiyya mai hankali, ta san illar zina, ta san girman zunubinta amma sai fitinar sha’awa ta sa ta afka cikin wannan bala’i.

Domin kaucewa faɗawa makaranatar Shaiɗan, dole ne duk wani matashi da yake fuskantar barazanar sha’awa ya yi la’akari da wasu dokoki da addini ya shar’anta masa, sannan kuma ya yi amfani da dabaru wanda za su taimaka masa. Mu sani cewa fitinar sha’awa halittace kuma a zuciya ta ke, daga cikinta ta ke bijirowa, don haka mai son ya iya danne fitinar sha’awarsa duk lokacin da ta taso masa, sai ya fara da gyara zuciyarsa tukunna.

Ana gyara ta ne ta hanyar cikata da kyawawan tunani da yanke duk wata igiyar mummunan tunani daga cikin ta da goge mazaunin duk wani mummunan shauƙi. Daga nan sai kyautata ɗabi’u da halaye da ayyuka, duk wata ɗabi’ar wani hali ko wani aiki da mutum ke yi indai bamai kyau ba ne, to yin watsi da shi zai qara haskaka masa zuciyarsa.

Kyawawan ɗabi’u sun haɗa da yawan murmushi, taimakawa ‘yan’uwa, makwabta da abokai, gaskiya da riƙon amana da sauransu. Kyawawan ayyuka sun haɗa da taka tsan-tsan wajen tsaida addini, duk abin da aka sa ba daidai ba ne a addinance sai a yi ƙoƙari a barshi komai daɗinsa ko ribarsa. Yawan sanya Allah a zuciya da yin zikiri. Kiyaye ibada yana daga cikin maganin da yake wa mutum kandagarki daga fitinar sha’awa.

Lallai ne ’yan’uwa mu kula da kiyaye sallolin farilla da nafila da yawaita karatun Alƙur’ani da sauran azkar.

Haka kuma dole su kansu iyaye su kula da rayuwar ‘ya’yansu matasa maza da mata, domin kare su daga wannan bala’i.

Daga Mai kishin matasa; 09070905293.