Amnesty ta bayyana damuwa kan makomar aikin Jarida a Nijar

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International, ta bayyana fargaba a game da makomar ‘yancin aikin jarida a Jamhuriyar Nijar, bayan da kotu ta yanke hukuncin ɗaurin talala a kan wasu ‘yan jaridu biyu saboda sake wallafa labarin da wata jarida ta wallafa dangane da matsalar fataucin miyagun ƙwayoyi a ƙasar.

A ranar 3 ga wannan wata na Janairu ne kotu a Yamai ta yanke hukuncin ɗaurin talala a kan Samira Sabou da Moussa Aksar saboda sun sake wallafa labaran da wata Cibiya da ke Geneva mai suna Global Initiative Against Transnational Organized Crime (GITOC) ta buga, da ke cewa mahukunta a ƙasar ta Nijar, sun sake miƙa miyagun ƙwayoyin da jami’an tsaro suka ƙwace daga hannun wasu fatake.

Ma’aikatar shari’a ta yi amfani da dokar da ke hukunta masu aikata laifi ta yanar gizo ne domin ɗaure ‘yan jaridar biyu, hukuncin da Ousman Diallo, mai bincike a ofishin ƙungiyar ta Amnesty na yammacin Afirka ya bayyana a matsayin wani yunƙuri na tauye ‘yancin yaɗa labarai a ƙasar.

Ɗaya daga cikin waɗanda a ka yanke wa hukuncin wato Samira Sabou, ita ce shugabar ƙungiyar ‘Association of Bloggers for Active Citizenship ABCA’ wato ‘ƙungiyar masu wallafa labarai da sauran abubuwan wayar da kan jama’a ‘yan kishin ƙasa a kafofin intanet’, yayin da Moussa Aksar ke matsayin mamallakin jaridar L’Evenement kuma shugaban Cibiyar Norbert Zongo da ta ƙunshi ‘yan jarida masu bincike a yammacin Afirka wato CENOZO.