Bala Chamo ya zama Shugaban ALGON na Arewa

Daga BILKISU YUSUF ALI

An zaɓi Shugaban ƙaramar hukumar Dutse da ke Jihar Jigawa, Hon. Bala Usman Chamo, a matsayin Shugaban Ƙungiyar Ciyamomin Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Nijeriya (ALGON) mai kula da yankin arewacin Nijeriya.

Hon. Chamo, wanda kuma shi ne Shugaban ALGON na Jihar Jigawa, an zaɓe shi shugaban ƙungiyar na Arewa ne a ranar 15 ga Janairu, 2022, inda shugabannin ƙananan hukumomin suka nuna masa yaƙininsu na kawo cigaba ga yankin Arewa bisa la’akari da ƙwazonsa wajen sauke nauyin da ke kansa.

Wata majiyar ƙungiyar ta ce, “Hon. Chamo ya yi ayyuka na raya garin Dutse da kuma al’ummar da ke wannan ƙaramar hukumar kuma a wasu lokutan ma har da maƙwabtan jihar.

“Akwai yaƙinin zai kawo ci gaba da yin duk abin da ya dace, don ci gaba da kawo al’amuran ci gaba a cikin zauren da ma jihohin Arewan da ƙasa bakiɗaya.”

Binciken Wakiliyar Blueprint Manhaja ya nuna cewa, al’umma Jihar Jigawa sun nuna jin daɗinsu da kuma taya Shugaban Ƙaramar Hukumar murna, sannan sun ce lallai an ɗora ƙwarya a gurbinta, don Chamo mutum ne mai bin hanyoyi da nuna ƙwarewa wajen iya mulki da kyautatawa al’ummarsa da haƙuri da juriya. Don haka ya taushe dukkanin ’yan adawa a jihar.