Da abokin daka akan sha gari

Daga SAMINU HASSAN

Kamar yadda muke ji yau da kullum daga bakin masana, cewa babu wata ƙasa a duniyar nan da za ta samu cikakken ci gaba, ba tare da bunƙasa yankunanta na karkara ba, muna iya ganin shaidu na zahiri don gane da hakan a nan ƙasar Sin.

Mahukuntan ƙasar Sin sun jima da fahimtar muhimmancin kawar da ƙangin talauci da raya karkara, a matsayin babban jigon gina ƙasa, tare da tabbatar da ba a bar wani ɓangare na alummar Sinawa a baya ba. Kaza lika da yake yankunan karkara na taka muhimmiyar rawa wajen gina ƙasa, ta hanyar samar da nauo’in cimaka, kama daga hatsi, da kayan lambu da ’yayan itatuwa, gudummawar sassan na karkara na kan gaba wajen tabbatar da samar da isasshen abinci ga ɗaukacin yankunan kasar, hakan ya sa har kullum, gwamnatin Sin ke ƙara azama wajen ganin yankunan karkara sun kara azamar fita daga talauci, da samun kyakkyawar rayuwa.

Bahaushe kan ce Da ruwan ciki a kan ja na rijiya, har kullum mahukuntan Sin na dagewa wajen ganin yankunan karkarar ƙasar sun samu dukkanin tallafin da suke buƙata na raya sanao’i, da inganta damammakin samar da ilimi, lafiya da sauran ababen more rayuwa.

Wannan ne ma ya sa duk da yawan ayyukan dake gaban shugaban ƙasar Xi Jinping, wanda kuma shi ne babban sakataren kolin JKS, ya kan ware lokuta musamman domin ziyartar yankunan karkarar ƙasar Sin, ya gana da jamaar yankunan, ya ji koken su, da yanayin rayuwar su, da irin ci gaban da suka samu ƙarƙashin manufofin wanzar da ci gaba.

Wani abun birgewa game da manufar gwamnatin Sin mai ci shi ne yadda take ƙarfafa gwiwar yankunan karkara, wajen tashi tsaye domin dogaro da kai. Cikin kalaman shugaba Xi Jinping ya taba bayyana cewa Idan har burin mu shi ne kallon na sama da mu, muna neman a taimaka mana, muna ƙorafin rashin samun dama kamar saura, ta yaya za mu iya samun karfin gwiwar yaƙar fatara?”

Ziyarar da shugaba Xi Jinping ya kai ƙauyen Yongfeng na lardin Sichuan a cikin makon nan, ta shaida wannan muhimmiyar manufa, domin kuwa yayin da yake rangadi a ƙauyen na Yongfeng, ya nazarci yadda ake kara azamar kyautata samar da kayan noma na zamani, da matakan bunƙasa samar da hatsi a yankin, da ayyukan raya karkara, da matakan daƙile yaɗuwar annobar COVID-19.

Wannan ziyara ta shugaba Xi, ta dada shaida burin mahukuntan Sin, na yin tafiyar samar da ci gaba tare da dukkanin yankunan kasar, ta yadda kowa zai ci gajiya daga alfanun manufofin kawar da talauci, da wanzar da ci gaba, da gina alumma mai makomar bai ɗaya ga kowa, kamar dai yadda a kan ce Da abokin daka a kan sha gari.