Xi Jinping ya rubuta wasiƙa ga mahalarta taron ƙarawa juna sani na jam’iyyu shida dake Kudancin Afirka da suka kafa makarantar Julius Nyerere

Daga CMG HAUSA

Jiya Laraba, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya rubuta sako ga dukkan mahalarta taron sanin makamar aiki na jami’ai matasa na jam’iyyu shida dake kudancin nahiyar Afirka, waɗanda suka kafa makarantar koyar da harkokin shugabanci ta Julius Nyerere.

Xi ya ce, neman cimma muradun ci gaba, da farfaɗo da al’umma da samar da alfanu ga jama’a, na buƙatar jajircewar zuriyoyin al’umma. Kara gina duniya mai kyakkyawar makoma, na buƙatar mu’amalar ƙasa da ƙasa.

Xi ya jaddada fatansa cewa, ya dace waɗannan jami’an su dauki nauyin dake wuyansu, da nuna kwazo wajen raya sha’anin ƙarfafa zumunta tsakanin Sin da Afirka, a ƙoƙarin bayar da gudummawarsu wajen gina al’ummomin Sin da Afirka masu kyakkyawar makoma ta bai daya.

Kwanan baya, aka gudanar da taron sanin makamar aiki tsakanin jami’ai matasa na jam’iyyu shida dake kudancin nahiyar Afirka, wadanda suka kafa makarantar koyar da shugabanci ta Julius Nyerere tare a ƙasar Tanzaniya. Taron, mai aken “Sabon ci gaba a sabon zamani: Mu’amala da haɗin-gwiwa tsakanin jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin da jam’iyyu shida dake kudancin nahiyar Afirka”, ya samu halartar wasu jami’ai matasa 120, waɗanda suka gabatar da wasiƙa ga shugaba Xi a ƙarshen taron, don bayyana aniyarsu ta ci gaba da yauƙaƙa zumunta da zurfafa haɗin-gwiwa tsakanin Sin da Afirka.

Fassarawa: Murtala Zhang