Sin ta yi kira da a kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Tsakiyar Afirka

Daga CMG HAUSA

Dai Bing, mataimakin zaunannen wakilin ƙasar Sin a MƊD ya yi kira da a kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tsakiyar Afirka.

Dai Bing ya faɗi haka ne yayin wani taron kwamitin sulhu na MƊD kan batun yankin tsakiyar Afirka da aka yi a jiya, inda ya kuma nuna cewa, tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin na tsakiyar Afirka, yana amfanawa cikakken tsaron nahiyar Afirka.

Kuma ƙasar Sin na tsayawa tsayin daka wajen goyon bayan ƙasashen da ke yankin da su yi ƙoƙarin kiyaye ikon mulkin ƙasa da cikakkun yankunansu. Ya ce wajibi ne kasashen yankin masu ruwa da tsaki su daidaita saɓani ta hanyar diplomasiyya da siyasa, a kokarin tabbatar da haɗin kansu da kwanciyar hankali a yankin.

Dai Bing ya ƙara da cewa, ya kamata ƙasashen duniya su ƙara ba da tallafin kuɗi da na fasaha ga ƙasashen yankin domin yaki da ta’addanci, da mara musu baya wajen tsara shirin kwance damara, a ƙoƙarin dakile yaduwar ta’addanci.

Haka kuma ya kamata a goyi bayan ƙasashen yankin wajen kyautata kwarewarsu ta tafiyar da harkokin kasa, da taimakawa al’ummomi fita daga ƙangin talauci, da kuma daidaita batun haka da cinikin albarkatun halittu ba bisa doka ba, ta yadda za a kawar da tushen rikice-rikice.

Fassarawa: Tasallah Yuan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *