Da dumi-duminsa- Da yammacin yau Asabar Gawar Tahir Fadlallah za ta iso Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano

A yau ne ake shirin aiwatar da Jazaizar babban dan kasuwan nan Tahir Fadlallah mamallakin Hotal ɗin Tahir da ya rasu jiya Juma’a, rasuwar Marigayin dai ta girgiza al’ummar Kano da ma duniya baki ɗaya,

Marigayi Tahir Fadilallah ya rasu ne a wata cibiyar lafiya da ke birnin Beirut na kasar Labanon.


Rahotanni sun ce tun a ranar 15 ga watan Afrilun da muke ciki ne aka kwantar da shi a sashen kulawa da wadanda ciwonsu ya yi tsanani na cibiyar,

A wani sako da iyalan mamacin suka aikewa Freedom Radio sunce a na sa ran isowar gawarsa a filin jirgin Malam Aminu Kano, da misalin karfe 3 na yammacin yau Asabar. Za ku ma a binne shi ne a maƙabartar ƙwarori da ke titin sansanin Alhazzai na Kano (Hajji Camp)

Marigayin yana da shekaru 74 yana da ‘ya’ya 5 da jikoki 10, daga cikin ‘ya’yansa akwai dansa Muhammad Mahmud shugaban rukunin Tahir,

Idan za a iya tunawa dai a ranar 24 ga watan Afrilun 2020 ne aka tafi da Fadlallah daga Kano, bayan da ya fara rashin lafiya, wanda ake zargin cutar kwarona ce, kafin rasuwar Marigayin shi ne shugaban Kwarori mazauna Nijeriya.

Kazalika yana cikin fitattu mutane 82 da gwamnatin Kano ta karrama, a shekarar 2017 kan irin gudunmawar su wajen daukaka jihar,

Tuni fadar shugaban kasa ta bayyana alhininta, kan rashin Marigayin a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari Garba Shehu ya fitar, ya bayyana rasuwar Tahir a matsayin babban rashi ga al’umma duba da irin gudunmawar da ya bayar a rayuwarsa,

Ita ma gwamnatin Kano tuni ta mika sakon taaziyya ga iyalai da ‘yanuwa da abokan arziki, a cikin wata sanarwa da muƙaddashin gwamnan Kano, Dr. Nasir Yusuf Gawuna ya fitar, sanarwar ta bayyana marigayin a matsayin gwarzo wanda ya jajirce a matsayin gwarzo wajen bunkasa tattalin arzikin jihar Kano, Gawuna yayi addu’ar Allah ya gafartawa Fadlallah da sauran al’ummar musulmi baki daya.

Har yanzu dai al’umma na cigaba da nuna sakon alhininsu kan wannan rashi musamman a kafafen sadarwa na zamani.

By Editor