Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Daniel Bwala, mai ba Shugaban ƙasa Bola Tinubu shawara na musamman kan harkokin sadarwa da manufofi, ya bayyana cewa wasu daga cikin masu sharhi a kan batutuwan ƙasa a kafafen sada zumunta a Nijeriya na iya kasancewa suna da wasu matsaloli na lafiyar ƙwaƙwalwa.
Mista Bwala ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels yayin da yake mayar da martani kan jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ziyarar da Mista Tinubu ya kai kwanan nan zuwa ƙasar Faransa na da nasaba da lafiyarsa.
Sai dai ya ce, saɓanin jita-jitar da ake yaɗawa, Mista Tinubu ba ya Faransa don neman magani ba, sai dai don wata ziyara ta aiki.
“Wani lokaci a kafafen sada zumunta, mutum zai dinga wallafa rubuce-rubuce; ba ma a san ko wanene ba; watakila ma yana da wata matsalar ƙwaƙwalwa ne. Abin da kawai kake gani shine wasu bayanai suna yaɗuwa.
“Shugaban kasa bai je ganin likita ba; yana cikin wata ziyara ta aiki kuma muna ci gaba da wallafa ayyukansa,” inji shi.
Mai ba shugaban ƙasa shawarar ya kuma caccaki Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, saboda sukar da yake yawan yi wa gwamnatin Tinubu.
