2027: Babu hannunmu a kakkafa allunan tallar Tinubu da Shettima – Fadar Shugaban ƙasa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Fadar Shugaban ƙasa ta lura, tare da nuna damuwa yadda ake samun ƙaruwar allunan talla a wasu garuruwan da ke tallata

Yaƙin neman zaɓen Shugaban ƙasa, Bola Tinubu da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima a 2027.

Abin ma har da wanda aka yi manyan alluna na Tinubu da Maiɗakinsa aka kakkafa a Abuja.

“Duk da dai shugaban ƙasa da mataimakinsa na miƙa godiya ga ɗinbin magoya baya da ke nuna musu ƙauna a faɗin ƙasar nan, sai dai kuma ba za su amince wa a riƙa saɓawa ko karya dokar ƙasa ba.

“Dokar zaɓe ta haramta duk wani nau’i na yaƙin neman zaɓe na 2027. A matsayinmu na shugabanni masu bin doka da oda, Shugaba Tinubu da mataimakinsa Shettima ba sa goyon bayan duk wani mataki da zai saɓa wa tsarin kasa da shimfiɗar da doka ta a kasa komai kyan sa kuwa.

“Har sai hukumar zaɓe ta fidda jadawalin zaɓukan 2027, shugaban ƙasa bai amince da wani ko kungiya su fara yi masa kamfen ɗin zarcewa ba kowacce iri. Ko a kowacce irin kafa ce kuwa, tun saga talbijin, yanar gizo, rediyo da kuma kafa alluna.

“A dalilin haka muna gargaɗin masu yin haka da su janye daga haka su kima shiga taitayinsu tun da wuri.”

By ukarofi