Dakatar da RTEAN da Gwamna Sanwo-Olu ya yi a Legas abin takaici ne – Ƙungiya

Daga BASHIR ISAH

Shugabancin Ƙungiyar Masu Motocin Haya ta Nijeriya (RTEAN) ya ce sam ba daidai ba ne dakatar da reshen ƙungiyar na Jihar Legas da gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu ya yi tare da naɗa kwamitin riƙon ƙwarya mai mambobi 35.

Shugabancin RTEAN ya bayyana haka ne cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar don bayyana rashin jin daɗinsa kan matakin da gwamnan na Jihar Legas ɗin ya ɗauka.

Ƙungiyar ta ce akwai rassan RTEAN sama da 300 a Legas, kuma don an samu rashin jituwa a tsakanin biyu daga cikin rassan bai kamata hakan ya zama silar dakatar da ƙungiyar a jihar baki ɗaya ba.

A cewar sanarwar, RTEAN ƙungiya ce mai cikakkiyar rijista, kuma mai kundin tsarin mulki ta yadda a duk lokacin da wata matsala ta taso mata, a ƙyale ta ta yi amfani da dokokinta wajen magance matsalar tata.

Kazalika, sanarwar ta ce babu inda dokar ƙungiya ta nuna gwamnan ko waninsa zai iya shigowa ya zartar da wani mataki ga ƙungiyar da mambobinta alhali ƙungiyar na da zaɓaɓɓun shugabannin da su ne doka ta ɗora wa alhakin gudanar da komai.

Ƙungiyar ta ce idan har ya kama babu makawa sai gwamnan ya sa hannu don samun maslaha, to, kamata ya yi ya sa a binciki rassa biyun da ake da matsala sannan a kama waɗanda suka haddasa fitinar don su fuskanci hukunci.

Ta ce lamarin da takaici ganin kwamitin riƙon da gwamnan ya kafa ya ƙunshi har da waɗanda ake kyautata zaton da hannunsu cikin rikicin da ke tsakanin rassa biyun da rikicin ya shafa.

Daga nan, shugabancin RTEAN na kasa ya roƙi gwamnatin Legas da ta bar masa batun don ya magance matsalar daidai da tanadin dokar ƙungiyar.

Kazalika, ya roƙi Gwamna Sanwo-Olu da ya janye jami’an tsaron da ya sa aka girke a ofishin ƙungiyar.