Ba na tare da Wike a kan cire Ayu — Gwamna Ortom

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Benuwai, Samuel Ortom ya musanta rahotannin da ke cewa yana goyon bayan tsige Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Dr Iyorchia Ayu daga muƙaminsa, inda ya ce babu yadda za a yi ya goyi bayan cire wanda ya taimaka aka naxa.

Jaridar TheCable ta rawaito cewa Ortom ɗin ya kuma ce yana da yaƙinin Mr Ayu zai jagoranci jam’iyyar ga nasara a zaven baɗi.

Waɗannan kalaman sun ci karo da matakin da ɓangaren Gwamna Wike wanda Ortom mambe ne, da ke neman lallai sai an cire Iyorchia Ayu matuƙar ana son zaman lafiya a Jam’iyyar PDP mai adawa.

Martanin gwamnan na zuwa ne bayan da wata ƙungiyar ci gaba a jihar Binuwai, Jemgbagh Development Association ta yi zargin cewa Gwamna Ortom na shirya kutungwilar cire ɗan uwansa na Jihar Binuwae wato Mista Ayu.

Kawunan ‘yan PDP sun rabu, tun bayan da aka zaɓi Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, inda ɓangaren Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike yake ta gindaya sharuɗɗa daban-daban idan har ana son ya ba da goyon baya a zaɓen da ke tafe a Nijeriya cikin shekara mai zuwa.