Daga AMINA YUSUF ALI
Barkanmu da haɗuwa a wani sabon makon a wannan jarida tamu ta Blueprint Manhaja. A wannan mako za mu kawo muku maudu’in nan mai matuqar ban mamaki na satar hanyar wasu matan auren ko ma na ce zina. A ƙasar Hausa ba ƙaramin abin mamaki ba ne da kunya a ce yau an kama matar aure tana zina. Abu ne da yake wahalar samu, amma akwai.
Na zavi na yi wannan rubutu saboda faɗakarwa ɓangaren maza da na mata a game da dalilan da suke jawo zinar matan aure, da kuma haɗarorin da ke tattare da ita da yadda za a magance. Domin a zaman aure, maza na satar hanya, haka mata na yi. Amma yayin da aka kama mace da cin amanar aure, da wuya namiji ya cigaba da zaman da ita.
Amma ita mace za a iya ba ta haƙuri ta zauna da shi. Domin zinar matar aure rusa gida take gabaɗaya. Shi namiji Allah ya halicce shi don mata fiye da ɗaya, zai iya yin satar hanyar kuma ya voye wa matarsa, kuma ya cigaba da faranta mata ta rayu cikin farin ciki. Yayin da ita kuma mace saboda namiji guda aka yi ta, sai kaga da zarar ta samu wani a waje, da wahala kuma hankalinta ya cigaba da tsayawa a kan wancan mijin nata na sunna.
Dole sai ya karkata, ko tana so, ko ba ta so. Mace ba a yi zuciyarta don maza barkatai ba. Ala ayyi halin dai, zinar ma’aurata da ma marasa auren, haramun ce, kuma tana rusa gida ta zub da mutunci.
Me yake sa matan aure yin zina?
Kamar yadda muka sani, zina tana daga manyan laifuka, alkaba’irai waɗanda Allah ya tanadar wa azaba mai tsananin uƙuba. Wanda har a duniya ma an tanadi hukunci mai zafi a gare su. Sannan kuma tunda Allah ya halicci ɗan adam da dabbobi da bukata ta ‘yanadamtaka, kamar yunwa, ƙishirwa, da sauransu haka ya halicci ɗanadam da wannan buƙata ta jima’i. Wato kowanne jinsi yana buƙatar ɗan uwansa.
Amma sai ya banbanta mutum da dabba ya shar’anta aure a matasayin wata hanya da mutane za su samu biyan wannan buƙata. Sai dai a son rai irin na ɗanadam da rashin tsoron Allah da godiya gare shi, shi kuma yake sa ya yi zina. Amma kamar yadda na faɗa a baya, dukka suna da laifi a wajen Allah, amma kuma ta matar aure ta fi illa nesa ba kusa ba.
Sai dai kuma wani bincike ya nuna cewa, mafiya yawan zina ta maza ce. Amma kuma ƙarfe ɗaya fa Hausawa sun ce ba ya ƙara shi kaɗai. Ga wasu daga cikin dalilan da suke sa matar aure bin wasu mazan:
· Dalili na farko, akwai zancen rashin tsoron Allah da rashin miƙa masa lamurra. Duk abinda aka ce Allah ya hana, a matsayinka na musulmi ka aikata, to akwai alamar ba ka tsoron Allah. Don kauce wa zunubi yana nuna tsoron Allah.
· Son zuciya. Akwai matan da babu abunda mazajensu na aure suka rage su da shi na daga kulawa ta fannin soyayya da ba da kuɗi, amma duk da haka suna bin wasu mazan.
· Talauci; Akwai matan kuma da mazajensu masu tafiye-tafiye ne, suna barinsu ba kuɗin kashewa da za su gudanar da a’lamuran rayuwa kamar ci da sha, ko sabulun wanka da wanki da sauransu. Ko kuma ma mijin yana nan a gari, ko yan da shi, ko bai da shi, amma sai ka ga ya bar ta haka. Wata ma ga yara ta tara. Irin waɗannan mata buƙatarsu kan ja su ga aikata zina. Ko su je rokon namiji ya yi amfani da damar ya neme ta da zina. Wani ma ɗan uwanta ne ko na mijin ko abokinsa. Wasu kuma, mijin yana mata amma kwaɗayin abin duniya yana angiza ta ga bin maza.
· Rashin kulawa: Rashin kulawa daga namiji ta fannin ɗaukar nauyi, da raha, da soyayya duk suna sa ta yi sha’awar mu’amala da wani namijin wanda ya kula ta a waje. Namijin da ba shi da mu’amala da mace mai kyau yana barinta ta yunwar neman kulawar. Kuma wata idan idonta ya rufe za ta nema ko ta halin ƙaƙa. Chatting ne, a kanti ko kasuwa ne, wajen auki, makwabta, abokin miji, babu masaniyar a inda abin zai faru. Sai abu ya fara kamar wasa, sai ya juye ya zama babba.
· Neman mafita: Akwai matan da suke fuskantar cuzgunawa a wajen mijinsu, ko a wani fanni na rayuwa. To ba ta samu fuska ko fahimtar juna da mijinta ba balle ta samu ta sanar da shi. Wata ma hira wannan ba ya yi da mace, sai dai majalisa. To kuma ɗabi’ar ɗanadam yana son idan abu ya dame shi ya sanar da wani. Sai ka idan ba a dace ba wata har da almajirin gida ko wani mai aiki za ka ga tan hira tana gaya masa matsala. Ko abokin aiki ko ma wanda ba ta sani ba a catin. Shi ma wataƙila hakan ya sa ya saki jiki ya fara gaya mata tasa matsalar, ba za su ankara ba kawai su ji sabo da shaƙuwa mai tsanani sun qullu a tsakaninsu har ma so ya fara shiga. Daga nan sai su ji suna son su bunqasa soyayyarsu ta hanyar saduwa da juna, tun ana yi a voye, har a fara a bayyane asiri kuma ya tonu rai ya vaci.
· Roƙo: Mace mai roƙon maza tana zubar da ƙimarta har su samu ƙofar nemanta da iskanci.
· Rashin kamun kai da son kula maza: Mace mara kamun kai tana buɗe ƙofa ga maza marasa kamun kai da tsoron Allah su neme ta da alfasha.
· Rashin samun gamsuwa a gidan aure: Rashin samun gamsuwa a gidan aure kan iya jefa mace ta fara cin amanar mijinta na aure. Bincike ya nuna cewa, mata da dama ba sa cin amanar aure saboda matsalar jima’i. Sun fi yi saboda neman soyayya da kulawa. Rashin abokin hira da kaɗaici da sauransu. Mace a rayuwarta ba ta son kaɗaici ko kaɗan. Ta fi son a ce yau ga wani wanda za su samu fahimtar juna, har ma ta dinga gaya masa damuwarta. Matar da mijinta ya bar ta a kaɗaici, ta fi saurin ba da haɗin kai wajen hira da mazan da ba nata ba, idan da tsautsayi kuma abin ya miƙa ya kai ga alfasha. Amma fa a sani, mace mai tawakkali da tsoron Allah, don mijinta ya yi watsi da ita fa ba ta neman mafita a wajen mazan waje.
A nan zan tsaya, za mu ci gaba a mako mai zuwa, idan rai ya kai. 08024859793.
