Tinubu ya gana da Kwankwaso a Faransa

Daga BASHIR ISAH

Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, a Paris, babban birnin ƙasar Faransa.

Bayanai sun ce Tinubu da Kwankwaso sun yi ganawar sirri bayan haɗuwar tasu inda suka shafe sa’o’i huɗu suna tattaunawa.

Majiyarmu ta ce tattaunawar tasu ta shafi yadda za a yi tafiya tare da Kwankwaso a gwamnati mai jiran gado kasancewar Tinubu na da ra’ayin kafa gwamnati ta haɗin kan ƙasa.

Kazalika, majiyar ta ce daga cikin batutuwan da suka tattauna har da batun shugabancin majalisar tarayya.

Wadanda suka halarci ganawar sun haɗa da Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila da Abdulmumin Jibrin wanda jigo ne a Jam’iyyar NNPP da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *