Bincike ya nuna yin waya fiye da minti 30 a mako na saka hawan jini

Masana kiwon lafiya sun gano cewa yin waya na sama da minti 30 a mako guda na haddasa ƙaruwar cutar hawan jini da kashi 12.

Rahoton da Ƙungiyar Likitocin Zuciya na Nahiyar Turai ta fitar a ranar Juma’a ya buƙaci jama’a da su takaita yin waya domin kare lafiyar zukatansu.

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa rahoton likitocin da aka wallafa a mujallar Digital Health yana nuna yin waya na sama da minti 30 a mako na ƙara barazanar kamuwa da cutar hawan jina da kashi 12 cikin 100.

Mujallar, wadda a mayar da hankali a kan yadda na’urorin zamani ke shafar lafiyar zuciya, ta ce hakan bai shafi yawan shekarun da mutun ya yi yana amfani da waya ko sanya waya a lasifika ba.

Farfesa Xianhui Qin na Jami’ar Aikin Likita tat Kudancin Guangzhou da ke ƙasar China, ya ƙara da cewa masu amfani da waya sun fi mara sa yi yiwuwar kamuwa da hawan jini da kashi 7 cikin 100.

Farfesa Qin ya a halin yanzu kusan biliyan 1.3 masu shekaru 30 zuwa 70 na da hawan jini, wadda ke iya kawo shanyewar barin jiki da kuma mutuwa farat-ɗaya.

Masanin ya bayana cewa, “Wayoyin hannu na fitar da maganaɗisun da ke ƙara haɗarin kamuwa da hawan jini bayan wani lokaci.

“Duk da haka yanayin amfani da waya da ke kawo hawan jini ya bambanta a tsakanin masu kira ko amsawa, da kuma masu tura saƙonni ko kuma yin wasanni da ita,” in ji Farfesa Qin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *