Dalilan da za su iya sa wa Ronaldo ya musulunta

Daga HARUNA BIRNIWA

Fitaccen ɗan kwallon ƙafar nan wato Cristiano Ronaldo ya jima yana nuna sha’awarsa kan wasu al’amura da suka shafi addinin musulunci, imma kai-tsaye ko ta wata hanyar daban. Yau na tattaro wasu muhimman alamu da suke ba da tabbacin gwarzon ɗan wasan na duniya zai iya karvar addinin Musulunci kafin kwantiraginsa ta shekara 2 ta ƙare da kulub ɗin Al-Nasser da ke ƙasar Saudiyya.

Idan Ubangiji Allah Yana nufin wani bawansa da alheri sai ya jarrabe shi da wata lalura ko naƙasa (inma ta jiki ko ruhi da abun da ya dangance shi) ko wata musiba ta karyewar arziki ko rashin nasara cikin al’amura domin ya shiryar da shi i zuwa wani gwadabe wanda da a ce lafiya ƙalau ne ba zai bi ba.

A irin wannan gavar ne nake ayyana naƙasar da CR7 ya yi a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus da Manchester City a matsayin wata hikima wacce za ta turo shi zuwa ga amsar kalmar Allah wato kalmar shahada.

Dalili na farko:- da Ronaldo ya yi nasarar ɗaukar kofin duniya a zuwansa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus da wataƙil ya ci gaba da zama a can tare da taka leda a matsayin mai jan ragama a jerin wasanni na kofin ‘Serie A’, amma da yake ƙaddara ce ke janyo shi daga duhu zuwa haske sai ya gaza tabbatar da ƙoƙarin da zai tabbatar da ƙudurin da ƙungiyar ƙwallon ƙafar ta siye shi a kai, don haka ko suka sayar da shi.

Dalili na biyu:- kodayake Hausawa sun ce idan basira ta qare wa kare, sai ya daina cizo ya koma tunkuyi, a lokacin da ƙungiyar Manchester City wacce take da ƙwararrun ‘yan wasa kusan fiye da kowacce ƙungiya a shekarar idan ka cire Liverpool suka neme shi tare da sanya masa maƙudan kuɗaɗe, amma sai CR7 ya ture tayinsu tare da amsa gayyatar ƙungiyar takwararta Manchester United kawai saboda wasu dalilai waɗanda su suka gaza duba su yayin da za su kore shi a ƙarshen shekarar nan. Shi kansa rashin nasarar zamansa a Man United babbar alama ce da take nuna Allah yana sake share masa hanyar zuwa ƙasa mai tsarki domin saduwa da wani al’amari mai ƙarfi.

Dalili na uku: ko a mafarki babu wanda ya taɓa tunanin benci zai karye da Ronaldo, sai dai kocin ƙasar Portugal ya tabbatar da hakan. Ko a gasar cin kofin duniya (World Cup) ma sai da waccan ƙaddarar da ana linke masa cikin rigar rashin nasara ta biyo shi, saboda duk wasan da aka fito da shi sai ya kasa kataɓus, da kuma an cire shi sai ka ga sauran ‘yan wasan sun fi ƙoƙari.

Tabbas ga duk mai zurfin tunani zai iya gane cewa akwai wani abu da Sarki Allah yake nufi da wannan bawa nasa, ko dai abunda muke tinani ko akasinsa, amma tabbas akwai tanadi da aya a cikin rayuwar Christiano.

Dalili na huɗu:- a bisa la’akari da shi wanda yake bayyana wa duniya ƙaunar addinin Islama da Ronaldo ɗin ya ke shi ne yadda yake zama ya saurari karatun Al-Ƙur’ani mai tsarki daga bakin abokin wasansa a tsohuwar ƙungiyarsa ta Real Madrid wato Mesut Ozil, har a wasu lokutan ma shi yake neman da ya karanta masa suratul Fatiha saboda yanda yake jin daɗi tare da samun kansa cikin nutsuwa da yanayi mai kyau yayin saurare.

Dalili na biyar: na zaɓi na rufe rumbun dalilan da suka sanya nake jin cewa addinin Musulunci zai yi babban baƙo da zayyano kyawawan halayen Ronaldo waɗanda ko wanda aka haifa a cikin addinin musuluncin ne ya same su haƙiƙa ya kai a yaba masa.

Shi dai CR7, ya kasance mutum mai tausayi. A nan muna iya tuno yanda ya siyar da takalmin zinarensa ya kuma sadaukantar da kuɗin ga al’ummar ƙasar Falatsinu, sannan ya siyar da kyautar Balon D’or ɗinsa ta shekarar 2013, inda ya saka kuɗin cikin gidauniyar ‘Make a Wish Foundation’. Bayan haka, ba ya yin zane a jikinsa wato ‘tattoo’ kuma ba ya shan giya, hakazalika, yana ba da jini ga majinyata kuma ba ya neman mata.

Ƙididdiga ta nuna shi ne ɗan wasa daga cikin ‘yan ƙwallo ko mawaƙa, ko ‘yan fim da ‘yan tsere da sauran duk nau’ikan motsa jiki da ya fi bayar da tallafi domin taimakon yara da mata da masu ƙaramin ƙarfi. Lalle ko zuwansa ƙasa mai tsarki zai sake ba shi damar cuɗanya a cikin musulmai da sake fahimtar kyawawan tadoji na addinin musulunci.

Haruna Birniwa marubuci ne, ɗan siyasa ne kuma mai fashin baƙi a kan al’amuran yau da kullum. Ya rubuto daga jihar Jigawa.