Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Ayyuka David Umahi ya fayyace matakin da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka na soke kwangilar da gwamnatin da ta gabata ta bai wa kamfanin Julius Berger na gyaran hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Zaria zuwa Kano.
Yayin da yake tofa albarkacin bakinsa game da batun soke kwangilar, ministan ya bayyana cewa matakin ya ta’allaƙa ne kawai akan tsarin Gwamnatin Tarayya, bayan Julius Berger ya haƙiƙance a kan farashi, tare da yin watsi da muhimmin ayyuka.
Haka zalika, Ministan ya bayyana yadda kamfanin Infiouest International Limited ya samu kwangilar wannan aikin, inda ya bayyana cewa Julius Berger ya ƙi yin amfani da damar da gwamnati ta ba shi a lokacin da ake shirin sake bayar da kwangilar.
Ministan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da manema labarai a ofishinsa da ke Abuja.
Ya kuma yi amfani da damar wajen fayyace cece-kucen da ake yaɗawa dangane da sunan sabon kamfani mai sarrafa kwangilar hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Ya ce, kamfanin ya nemi a sake duba kuɗin aikin zuwa wani matakin da ya wuce abin da gwamnatin tarayya ta ga ya dace a aiwatar da shi.
A cewarsa, kamfanin ya buƙaci a sake nazari domin ƙara kuɗin faɗaɗa hanyar mai tsawon kilomita 165.5 zuwa Naira Biliyan 2.3 kan kowacce kilomita. “Saboda haka, bayan fiye da watanni tara na tattaunawa, da kuma ƙoƙarin da Julius Berger ya yi ya koma wurin, dole ne mu dakatar da kwangilar,” inji ministan.
Ya ce, kamfanin ya yi watsi da gayyatar da aka yi masa na shiga cikin shirin sake bayar da kwangilar bayan an buɗe dama ga ’yan kwangila.
