Tare da CHIROMA AMINU ASID
Sau da dama mutane na iya fuskanta wani yanayi na saurin jin fitsari bayan sahur. Hakan yana faruwa ne, saboda wasu dalilai na halitta da ɗabi’a, kamar haka:-
Shan ruwa da yawa lokaci guda:
Idan mutum ya sha ruwa da yawa a lokaci guda, ƙodojinsa za su riƙa tace ruwan da wuri. Hakan na sa yawan fitsari.
Shan kayan sha masu ‘caffeine’:
Shan abubuwan sha masu ƙarfafa fitsari (Diuretics), wasu nau’in abinci ko abin sha na iya sa fitsari ya ƙaru. Wannan ya haɗa kayan sha masu ‘caffeine MM’, kamar a shayi da kofi, kayan marmari masu ruwa da yawa kamar kankana, lemun zaƙi da sauransu. Shayi ko kofi na ɗauke da ‘caffeine’, wanda ke ƙara yawan fitsari, domin yana aiki a matsayin ‘diuretic’ (mai fitar da ruwa a jiki).
Cin abinci mai gishiri:
Gishiri na iya shayar da jiki ruwa, amma daga baya zai sa ƙodoji su fitar da shi da wuri. Hakan na ƙara yawan fitsari.
Yin sahur da kayan marmari masu ruwa da yawa:
Kayan marmari kamar kankana, lemo da kwakwamba suna da ruwa mai yawa wanda zai iya sa mutum jin fitsari da wuri, idan aka sha yayin sahur da yawa.
Sanyin iska ko yanayi:
Idan ka na zaune a guri mai yanayin sanyi, jiki ba ya rasa ruwa ta hanyar zufa. Don haka ya kan fitar da shi ta fitsari da wuri.
Yanayin ƙodar mutum:
Wasu mutane suna da ƙodar da ta ke aiki da sauri fiye da na wasu. Hakan na iya sa su fi saurin yin fitsari bayan sun sha ruwa da yawa.
Matakan kiyaye saurin fita fitsari bayan sahur:
Sha ruwa a hankali – Kada a sha ruwa da yawa a lokaci guda, sai a sha a hankali tun kafin sahur, domin jiki ya riƙa sarrafa shi sannu a hankali.
Rage shan shayi da kofi – Idan mutum yana shan shayi ko kofi bayan sahur, zai fi dacewa ya rage yawansu, domin guje wa yawan fitsari.
Guji yawan cin abinci mai gishiri – Idan abincin sahur ya ƙunshi gishiri da yawa, zai iya sa fitsari ya ƙaru. Za a fi dacewa a rage yawan gishiri a abinci.