Dalilin da ya sa na cire ‘ya’yana a makarantar gwamnati – El-Rufai

Daga WAKILINMU

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana dalilin da ya sa ya cire ɗansa Abubakar-Sadiq da ƙanwarsa Nasrine daga makarantar gwamnati.

El-Rufai ya ce ya cire ‘ya’yan nasa daga makarantar Kaduna Capital ne saboda dalilin tsaron dubban ɗaliban makarantar. Yana mai cewa gwamnatinsa ta samu rahoton cewa wasu ƙungiyoyin ‘yan fashin daji su uku na shirin kai wa makarantar hari don sace ‘ya’yansa.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da BBC Pidgin ya yi da shi, inda ya ce bayan Sadiq haka ma ya saka ƙanwarsa Nasrine a makarantar a lokacin da ta cika shekara shida kafin daga bisani dalilan tsaro suka tilasta cire yaran daga makarantar.

Kodayake dai bayanan gwamnan sun nuna cire yaransa daga makarantar na wucin-gadi ne.

El-Rufai ya ci gaba da cewa a halin yanzu dai yaran na karatu ne daga gida, rubuta jarrabawa kaɗai zai kai su makaranta har sai lokacin da sha’anin tsaro ya inganta.

Ya ce ko da a ce ma ‘yan fashin sun zo ba za su yi nasarar sace yaran ba saboda akwai wadatar tsaro, sai dai hakan zai jefa sauran yaran cikin haɗari. Tare da cewa, ya ɗauki matakin cire yaran ne bisa shawarwarin jami’an tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *