Matawalle ya kori masu ba shi shawara na musamman

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya sauke dukkan masu ba shi shawara na musamman daga muƙamansu.

Muƙaddashin Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Kabiru Balarabe ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Gusau da yammacin Asabar da ta gabata.

Sanarwar ta bayyana cewa dakatarwar ba ta shafi mai ba da shawara na musamman kan al’amuran tsaro ba.

Sanarwar ta nuna cewa, “Wannan shawarar ta zo daidai da yadda Gwamna Matawalle ya sauya sheƙa zuwa APC a baya-bayan nan domin ganin an zurfafa bincike don zaƙulo wasu haziƙan mutanen da za a bai wa muƙaman siyasar ba tare da la’akari da ɓangaren shugaban siyasa ba”.

Matawalle ya umarci duk masu ba shi
shawara na musamman da abin ya shafa su miƙa lamuran ofisoshinsu da kadarorin gwamnati da ke ƙarƙashin kulawarsu ga daraktocinsu ko jami’an akawu.

Bayan haka, Gwamnan ya yaba da gudummawar da waɗanda lamarin ya shafa suka bayar wajen tafiyar da gwamnati tare da cewa matakin ya fara aiki ne nan take.

By Editor