Buhari na da ‘yancin murƙushe masu neman a raba Nijeriya – Aikpokpo-Martins

Daga UMAR M. GOMBE

An bayyana cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari na da ‘yancin murƙushe masu ra’ayin ɓallewa daga ƙasa irin su Nnamdi Kanu da Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho.

Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi Na Ƙasa (NBA) na 1, John Aikpokpo-Martins, shi ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook a ranar Asabar da ta gabata.

Mr Aikpokpo-Martins ya ce ra’ayin kai wajen neman ɓallewa daga ƙasa abu ne da ya saɓa wa dokar ƙasa.

Ya ce waɗanda suka yi ra’ayin kansu wajen neman ɓallewa daga ƙasa hakan kuskure ne. Yana mai cewa babi na 4 na kundin tsarin mulki na 1999 da ya yi magana a kan ‘yancin ɗan-adama bai haɗa da ‘yancin neman ɓallewa daga ƙasa ba.

A ra’ayin nasa da ya wallafa, Mr Aikpokpo-Martins ya taɓo bambancin da ke tsakanin tsohon shugaban tsegerun Niger Delta, Ekpemupolo da aka fi sani daTompolo, da Boko Haram da kuma IPOB haɗa da gboho.

Idan dai za a iya tunawa, a Talatar da ta gabata aka sake gurfarnar da Nnamdi Kanu a gaban wata babbar kotun Abuja bayan da gwamnatin Nijeriya ta samu nasarar sake cafko shi daga ƙetare.

Shi kuwa Mr Igboho jami’an tsaro ne suka farmaki gidansa da ke Soka a Ibadan, babban birnin jihar Oyo a ran Alhamis da ta gabata sa’o’i 72 kafin gudanar da gangamin da ya shirya a Legas na neman kafa ƙasar Yarabawa.

A cewarsa Tompolo bai taɓa neman ɓallewa daga Nijeriya don kafa wata ƙasa ba, saɓanin Boko Haram da IPOB da kuma Sunday Igboho waɗanda baki ɗayansu suke da nufin ɓallewa daga Nijeriya don kafa wata ƙasa mai cin gashin kanta.

Don haka ya ce a dokance, babu wani shugaba da za a samu irin wannan na faruwa a ƙasa sannan ya yi sakwa-sakwa da lamarin don kuwa dokar ƙasa ta ba shi dama da ƙarfin murƙushe irin waɗannan mutane.

Aikpokpo-Martins ya bayyana cewa, abu ne da ba zai saɓu ba Buhari da ya yi sha rantsuwar kare kundin tsarin mulkin ƙasa wanda a cikinsa babu inda aka nuna a biya wa masu buƙatar ɓallewa daga ƙasa buƙatarsu, a ce ya saurari waɗannan mutane.

Ya ce irin wannan ra’ayi ya saɓa wa dokar ƙasa, kuma kundin tsarin mulki ya bai wa Shugaban Ƙasa ‘yancin murƙushe irin waɗannan mutane.

Don haka ya ce masu neman a raba Nijeriya babu wata kariya go goyon baya da za su samu a wajen kundin tsarin mulki, kuma babu wani amfani da hakan zai tsinana musu.