Tankar mai ta yi ajalin mutum 10 a kasuwar Ibadan

Daga WAKILINMU

Bayanan da Manhaja ta samu daga Ibadan jihar Oyo, sun nuna an samu aukuwar haɗin tankar gas wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum goma.

Shaidu sun tanbatar cewa hadarin ya auku ne bayan da tankar gas da ta fito daga Ojaba a Ibadan ta saki hanya a Idi Arere ta kutsa cikin kasuwar Bode inda ta murƙushe mutane da abubuwan hawa.

Kazalika, shaidun sun ce galibin mutanen da tankar ta murƙushe ‘yan kasuwar Bode ne, kuma nan take wasu mutum goma suka ce ga garinku nan tare da jikkata wasu da dama.

An ga jami’an tsaro da na kwana-kwana a wurin da haɗarin ya auku suna zaman ko-ta-kwana gudun kada tankar ta kama da wuta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *