Hajjin 2021: Sai mai shaidar ‘permit’ zai shiga wasu muhimman wurare a Makka

Ma’aikatar Hajji da Umurah ta Saudiyya, ta ba da sanarwar cewa sai masu shaidar izini (Permits) kaɗai za a bari su shiga muhimman wurare a Makka da suka haɗa da; Harami da Mina da Arafat da kuma Muzdalifa yayin aikin Hajjin bana.

Ma’aikatar ta ce duk wanda aka kama da laifin take wannan ƙa’idar, za a ci shi tarar 10,000 SAR.

A cewar ma’aikatar wannan ƙa’idar za ta soma aiki ne daga gobe Litinin, 25 ga Zul-ƙadah, 1442, ta yadda in ban da alhazan da ke ɗauke da shaidar izini (Permits) babu wanda za a bari ya shiga Haram, ko Mina, ko Arafat, ko kuma Muzdalifa.

Ta ce duk maniyyacin da aka kama ya yi ƙoƙarin shiga waɗannan wurare ba tare da shaidar izini ba tarar 10,000 SAR za ta hau kansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *