Nijeriya za ta yi aiki da Pakistan wajen maganin masu tada zaune tsaye – Magashi

Daga BASHIR ISAH

Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi (mai murabus) ya sha alwashin Nijeriya za ta ci gaba da yin aiki tare da sojijin Pakistan a matsayin wani ƙoƙari na kawo ƙarshen fitinar masu tsattsaurar ra’ayi.

Janar Magashi ya bayyana haka ne sa’ilin da babban jami’in sojan Pakistan, Janar Nadeem Raza ya ziyarce shi a Hedikwatar Tsaro da ke Abuja a Juma’ar da ta gabata.

Magashi ya ce Nijeriya da Pakistan na da manufa iri guda ta fuskar neman daƙile harkokin masu tada ƙayar baya a cikin ƙasa.

Ministan wanda ya samu horo a wani ɓangaren aikinsa a ƙasar Pakistan ya ce duba da yadda ‘yan ta’adda a sassan duniya kan haɗa kai wajen aiwatar da harkokinsu da kuma barazana ga lumanar al’umma, akwaii buƙatar a yi aikin haɗin gwiwa tsakanin ƙashe don yi wa miyagun taron dangi.

Cikin wata sanarwar da da hadimin ministan, Mohammed Abduƙadir ya fitar, ministan ya ba da tabbacin cewa a shirye Nijeriya take ta tatsa daga hikimar da Pakistan ke da ita wajen magance matsalolin tsaro.

A nasa ɓangaren, Janar Nadeem Raza ya yi godiya da irin tarbar da ya samu a wajen ministan wanda a cewarsa hakan ya buɗe wani sabon shafi don sojojin ƙasashen biyu su yi aiki tare.