Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da an samu fashewar wani abu a Kaduna

Daga WAKILINMU

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna ta tabbatar cewa an samu fashewar wani abu a yankin Badarawa a jihar a ranar Asabar da ta gabata.

Bayanan ‘yan sanda sun nuna fashewar ta auku ne sakamakon wani makamashi da aka sarrafa cikin wasu gorunan madarar Viju guda uku.

Rundunar ta ci gaba da cewa, wasu yara su uku sun ɗauki waɗannan goruna a matsayin abin wasa a bisa rashin sani inda suka yi ta bugawa kamar ƙwallo wanda a ƙarshe gorunan suka fashe tare da ji wa yaran rauni.

Yaran da lamarin ya shafa su ne; Abubakar Aminu da Abubakar Abdullahi da kuma Abdullahi Abubakar.

Rundunar ta ce ba tare da ɓata wani lokaci ba an kwashi yaran zuwa asibitin koyarwa na Barau Dikko don yi musu magani inda ɗaya daga cikin yaran, wato Abubakar Aminu rai ya yi halinsa saboda raunin da ya ji.

Haka nan, ta ce an kula da Abubakar Abdullahi har ya samu sauƙi an sallame shi, yayin da Abdullahi Abubakar na ci gaba da samun kulawa a asibitin.

A ƙarshe, rundunar ta yi kira ga al’ummar Kaduna kan cewa babu buƙatar tada hankulansu saboda jami’anta na ko’ina a sassan Kaduna da kewaye don tabbatar da tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *