Dalilin da ya sa Tinubu ya ɓoye shirin cire tallafin mai daga jawabin rantsuwarsa – Shettima

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ɓoye aniyarsa ta cire tallafin man fetur daga jawabin rantsuwar kama aiki domin kauce wa matsin lamba daga masu adawa da matakin. Ya ce an ɗauki wannan shawara tun kafin Tinubu ya hau mulki, kuma ba mataki ne da aka ɗauka cikin gaggawa ba.

Shettima ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da gwamnoni a Legas a yayin bukukuwan babbar sallah da cikar gwamnatin Tinubu shekaru uku a kan karagar mulki. A cewarsa, shugaban ƙasar ya san cewa idan ya bayyana shirin cire tallafin a cikin jawabin rantsuwarsa, wasu mutane za su yi ƙoƙarin hana shi aiwatar da matakin.

Mataimakin shugaban ƙasar ya yabawa Tinubu bisa abin da ya kira jarumtakar shugabanci, yana mai cewa gwamnatin ta gaji tattalin arzikin da ke buƙatar manyan gyare-gyare. Ya ce maimakon ci gaba da jinkirta magance matsalolin da suka daɗe suna addabar ƙasa, gwamnatin ta ɗauki matakan da take ganin za su kawo sauyi mai ɗorewa ga tattalin arzikin Najeriya.

A nasa ɓangaren, Tinubu ya sake kare matakin cire tallafin mai, yana mai cewa ya ceci Najeriya daga faɗawa cikin matsanancin matsin tattalin arziki. Ya ce alamun farfaɗowar tattalin arziki sun fara bayyana, yayin da wasu gwamnoni suka yaba da sauye-sauyen da gwamnatin ta aiwatar. Shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC, Hope Uzodimma, ya ce gwamnoni sun gamsu da ayyukan shugaban ƙasar, suna ganin ya taimaka wajen dawo da ƙasar daga barazanar durƙushewar tattalin arziki zuwa yanayin kwanciyar hankali da ci gaba.

By ukarofi

Leave a Reply