Dalilin da ya sa zan zaɓi Abba Gida-gida

Daga MUHAMMAD SHAMSUDDEEN (Phd)

Abokina kuma takwarana Muhammad Shamsuddeen ya nemi na ba shi dalilina na zaɓar Abba Kabir Yusuf (AKY) a kakar zaɓen da take tunkaro mu a 2023. A taƙaice ga dalilaina nan a ƙasa. Ina fatan a dubi rubutuna da idon basira.

Da farko, ya kamata na yi tsokaci akan alaƙata da AKY. Tsakanina da Allah, ba ni da wata alaqa da shi face cewar garinmu ɗaya, Kuma addininmu ɗaya.

Ban taɓa amfana Kai tsaye da wani abu daga wajensa ba, Kuma ba na fatan wani abu na ƙashin kai ya haɗa ni da shi. Xungurungum, ko shi kansa Kwankwaso, ba ni da wata alaƙa da ta tava haɗa ni da shi, idan ban da adawar siyasa da na yi masa a shekarun baya, wadda daga baya ta rikiɗe ta koma soyayya.

Yadda aka yi adawata ga Kwankwaso ta koma soyayya wannan wani labarin ne daban. Amma dai gamsuwa da irin siyasarsa, da kuma son cigaban al’umma, su ne suka sa yanzu nake ra’ayinsa.

Na yi wannan bayani a sama ne domin kada wani ya ɗauka ina da wata riba ta son zuciya da ya sa nake son AKY ya ci mulkin Kano; ko ɗaya! Kawai dalilai ne na cigaban Kano, waɗanda na gamsu da su, suka sa nake fatan ya samu mulkin. Kuma zan zayyana su ɗaya bayan ɗaya a ƙasa.

Na farko, Abba Kabir Yusuf ya yi karatun zamani, tun daga matakin Difiloma, HND, PGD har zuwa digiri na biyu, irin na da ba na yanzu ba.

Wannan ya ba shi ƙwarewa ta zamani da kuma mafi ƙarancin ilimin gudanar da Gwamnati, musamman da yake Civil da Environmental Engineering ya fi ƙwarewa.

A ɓangaren ilimin addini, nan ma ya yi dai-dai gwargwado, tun da mahaifiyarsa jikan Goni Mukhtar ce da kuma Walin Zazzau Umarul Wali, wanda idan da ana gadon ilimin addini ma, da to AKY ya gaje shi.

Ko kakarsa ta ɓangaren Uba, Zainaba, ita kanta ‘yar Malam Sai’du ce, Limamin Huggalawa da ke ƙasar Bichi ta nan Kano.

Wannan ya ba shi damar samun kyakkyawan tubali na ilimin addini. Don haka ta fuskar karatu, ba shi da makusa a wajena.

Abu na biyu, AKY yana da ƙwarewa a mataƙa kan ayyukan Gwamnati daban daban, da kuma muƙaman siyasa. Ya fara aiki tun daga hidimar ƙasa (NYSC) a hukumar kare muhalli ta jihar Kaduna, sannan ya dawo kamfanin samar da ruwa na kano WRECA, sai kuma Ma’aikatar Ruwa ta Jihar Kano, in da ya taka matakai daban-daban.

A vangaren siyasa kuwa, AKY ya riƙe muƙamai iri-iri, tun daga matsayin Assistant Secretary na Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ma’aikatan Jihar Kano.

A shekarar 1999 -2003, lokacin AKY yana shekara 36 kacal, ya riqe mukamin PA na Gwamnan Kano, Wanda daga baya likkafa ta ci gaba zuwa matsayin SA na Gwamna a ɓangaren Shugabanci (Administration).

Wannan ya faru ne shekaru kaɗan bayan AKY ya gama digiri na biyu a ɓangaren shugabanci a Jami’ar Bayero. Tun lokacin ƙwazonsa ya sa yake ta yin gaba, inda yayi mataimakin na musamman na Ministan Tsaron Nigeria, daga 2003 zuwa 2006.

Yana wannan muƙamin ne aka zaɓe shi ya zama Publicity Secretary na Zauren PAs din Ministocin Nijeriya gabaɗaya, na wancan lokacin. Daga baya, AKY ya samu ƙwarewa a Diplomasiyya lokacin da ya zama Mataimaki na Musamman (SA) ga wakilin Nijeriya a yanking Dafur, a ƙasar Sudan a wancan lokacin.

A ɓangaren ilimi, AKY ya riƙe Shugaban Hukuma na National Institute for Educational Planning and Administration (NIEPA) wadda take a Jihar Ondo daga 2009 zuwa 2011. Wannan ya ba shi ƙwarewa a ɓangare gudanar da shugabanci da kuma tsarin ilimi.

Daga 2011, AKY ya sake dawowa harkar siyasa tsundum, in da ya riƙe mukamin sakataren tsare-tsare na Gwamnan Kano.

Sai dai bai daɗe a wannan muƙamin ba, ya samu mukamin Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri a ƙarƙashin Gwamnatin Dakta Rabiu Kwankwaso.

A wannan lokaci ne AKY ya taka rawar gani, wajen zartar da manyan ayyuka a Jihar Kano ta ƙarƙashin ma’aikatarsa. Waɗannan ayyuka sun haɗa da tituna, fadin samar na ƙasa, gidaje a rukuni daban-daban kamar birnin Kwankwasiyya, Bandirawo, da sauransu.

Haka nan harkar Sufuri a Jihar Kano ta bunƙasa matuƙa, ya samar da motocin Kwankwasiyya, da manyan motoci da ƙanana na ɗaukan ɗalibai, da Kuma tabbatar da kafuwar hukumar KAROTA domin magance matsalolin kan hanya.

Jihohi da yawa sun yi koyi da wannan hukuma ta KAROTA saboda ayyukan da take taimakawa da shi. Kusan ana ganin AKY a matsayin ɗaurin-ɓoye a Gwamnatin Dakta Kwankwaso daga 2011-2015.

Misali a watan July na 2012, Abba ne ya saka hannu a yarjejeniyar gina ƙananan gadoji (overhead bridges) guda 4 tare da manyan gadoji (flyovers) guda biyu shi da Mista Xia Jing na kamfanin TEC Construction, Kuma ya yi wa kamfanin kashedin da Lallai ya yi ingataccen aiki. Wannan kaɗan kenan daga cikin jajircewa irin ta sa. Wannan ɓangaren ƙwarewa kenan wajen ayyukan Gwamnati da na siyasa

Kano ta Dabo Cigari, Kano ta Dabo tumbin giwa; wannan kirarin duk bakanon da ya ji shi, sai ya yi alfahari. To shi fa wannan Ibrahim Dabo da ake cewa Kano tasa ce, kakan AKY ne.

Tun da Sarkn kano Ibrahim Dabo ta tsatsonsa aka sami Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi, Wanda ya haifi Galadiman Kano Yusufu, shi kuma ya haifi Muhammadu Bashir, shi Kuma ya haifi Dan Makwayyon Kano Yusuf wanda ya haifi Muhammadu Kabir, mahaifin AKY. A nan gurin akwai fa’ida guda biyu.

Ta farko, AKY yana jin Soyayyar Kano a jininsa, yana jin kamar Kano ta gidansu ce, don haka, zai yi iya ƙoƙarinsa ya ga ya kawo mata cigaba. Sabanin waɗannan mutanen da ba su san ƙimar Jihar ba, ballantana tarihinta.

Sun siyar da masallacin idi, sun rushe badala, sannan sun lalata masarautar Kano, sun mayar da ita ba komai ba, a ganinsu ba su da asara. Na biyu, akwai jinin mulki a jikinsa wanda a zahiri zai taimaka masa wajen ƙwarewa da salon mulki daban-daban.

Da yawa mutane suna alaƙanta salo da iya mulki na Marigayi Umaru Musa Yardua (Allah ya jikansa) da gidan da ya fito. Ni ina sa ran cewa AKY yana da wannan ƙwarewar.

Abu na ƙarshe shi ne, tsarin Kwankwasiyya da yake a kai. Babu shakka manufofi ko niyya su ne ginshiƙin kowanne irin aiki. Komai ƙoƙarinka idan tsarin da kake bi mummuna ne, to ba za ka yi abin kirki ba, sai ka shiga cikin “waƙadimna”. Amma idan niyyar mai kyau ce aikin baya baci, ko ya baci sai Allah ya datar da kai.

Wannan dalilai su ne suka sa nake kyautatawa Abba Gida-gida zaton cewa Kano za ta yi alfahari da mulkinsa. ‘Yayanmu da kannenmu za su ji daɗi, za a samu manyan aiyuka, ‘yan kasuwa, ma’aikata, ‘yan fansho, kowa zai yi walwala, kuma za a mayarwa da Kano martabarta a idon duniya.

Dakta Muhammad Shamsuddeen ya rubuto ne daga Jami’ar Bayero ta jihar Kano.
Lambar waya: 08181000300