Tsakanin Magoya bayan Ganduje da na Rarara: Kowa ya ci ladan kuturu

Daga HAMZA DAWAKI (Dawakin hikima)

Na lura da rabuwar kawunan mutane zuwa manyan gidaje uku, bayan samun ɓaraka tsakanin shahararren mawakin siyasar nan da ludayinsa yake kan dawo, wato Dauda Adamu Kahutu Rarara da Ubangidansa na siyasa, kuma Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Wato yayin da kaso na farko suke ganin shi Rarara shi ne ɗoɗar a kan turba, kuma shi yake da gaskiya a cikin dambarwar, kaso na biyu gani suke yi Gwamta Gandujen ne a kan gaskiya, kuma shi suke mara wa baya a harƙallar.

Yayin da kaso na ukun suka kasance ‘yan, ‘ku casu ba mai raba ku’. Wato a nasu ɓangaren, babu wani na zaɓen da za a iya ɗauka daga cikinsu.

Ba musabbabin rikicinsu nake son kalla ba, hali ko yanayin da ake ciki kawai zan kalla, wato rikicin. Ta yaya aka fara, ko me ya sa aka fara, ita ma wata doguwar maganar ce mai zaman kanta.

Abu mafi muhimmanci dai shi ne, a halin yanzu ta tabbata ana yin rikicin, kuma kowa ya fahimci ana yi ɗin. Tun da batutuwan sun karaɗe kafafen sadarwa. Har ma kowane ɓangare ya fara samun masu shigar masa faɗan.

Amma ni tawa matsayar akasin waccan ukun ce. Wato abin da ni nake gani, kawai irin abin nan ne da Bahaushe yake cewa wai “Abin da ka shuka, shi za ka girba” ne yake shirin faruwa da ɗaya ko ma dukkan sassan biyu.

Ko da ba yawan shekaru gare ni ba, amma da yake masoyin waƙa ne, na sha sauraren wakokin siyasa tun lokacin SDP da NRC, zuwa lokutan su UNCP da DPN da sauransu.

Amma ban tava jin wani mawaki da ya ɗauki matsaya irin ta Rarara ba. A iyakar sanina, Rarara ya ɗauki bashi, na cin mutuncin manyan mutane. Wanda babu wani mawaƙin ƙasar Hausa da ya taɓa ɗauka. Kuma a sunna irin ta rayuwa, dole ne kowa sai ya girbi abinda ya shuka.

Maganar gaskiya ita ce, kar ma mu yaudari kanmu. Rarara in ba Allah ne Ya ƙaddara masa gajeriyar rayuwa ba, sai rayuwa ta nuna masa bai isa ba, kamar yadda ya nuna wa waɗanda suka haife shi da waɗanda suka yi jika da shi kuma suke da riga ta kamala ko mulki ko dattijontaka ko dai wata daraja a idanun al’uma, cewa ba su isa ba.

Idan ka kasa fahimta ta, kowa ka yi nazarin yadda labaru da tarihin rayuwar magabatanmu suke tafiya:

Misali, idan aka ce an jefa mutum a rijiya bisa zalunci, lokacin da yake da rauni, a ƙarshen tarihin sai a ce maka wannan rarraunan ya dawo ya samu izza har sauran sun dawo ƙarƙashinsa.

Haka a hannu guda, idan aka ce maka, wani ya shahara a cin zarafin mutane a lokacin isarsa, da sannu a ƙarshen labarin za ka ji an ce maka, shi ma ya dawo wasu suna cinye nasa zarafin, ba kuma yadda zai yi.

Idan har yanzu ka kasa fahimta, dawo kusa da kai ka kalli rayuwarmu ta yau da kullum. Wato garinku ko unguwarku, ko ma layinku. Wannan yanayi kuma shi masu shirya labarai da fina-finai suke gini a kai. Domin shi ne abinda al’uma suka yarda yana faruwa.

Wannan wani tsayayye kuma tabbataccen tsari ko sunna ta rayuwa ce ta Duniya ta saba tafiya a bisa doronsa. Tsarin da masana suke cewa “Al Jaza”u min jinsil amal.” Ko “cause and effect” a Turance.

Don haka, idan har ka ce kai wannan ba zai faru da naka masoyin ba, tamkar yaudarar kanka kake yi.

Bisa wannan, wataƙila Gwanma Ganduje ya samu nasarar fara wasan kura da shi. Da yake shi dama abokin tafiyarsa ne. Shi ma yana ji da irin tasa isar. Wanda daga abin da ya bayyana a halaye da lafuzansa, mawuyacin abu ne wani ya taɓa shi, ya ci bulus. Sai ya mayar da biki, a salo irin na ramuwar gayya.

Idan hakan ta faru, an yi min daidai. Domin an fara sauke masa nauyi ne. Kafin shi ma mai saukewar a sauke masa. Idan kuma dukkansu sun wajiga juna, to sai mu ce, sun taya waɗanda za su sauke musu nauyin a nan gaba aiki.

Idan ma hakan ba ta samu yanzu ba dai, sai mu ce Allah Ya ba mu tsawon rai. Amma tabbas ita rayuwa tana tafiya ne a kan wani tsari tabbatacce: Abin da ka taya, shi take sayar maka.

Hamza dawaki mai nazari ne a kan al’amurran yau da kullum. Ya rubuto daga Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *