Yawan al’ummar Nijeriya kadara ce ga ƙasa – Isa Kwarra

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Kula da Yawan Al’umma ta Ƙasa (NPC), ta jaddada ƙudirinta na tattalin yawan jama’ar Nijeriya wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi ƙiyasin ya kai sama da mutum miliyan 216.

Hukumar ta ce za a yi tattalin yawan al’ummar ne domin tabbatar da fannin tattalin arziki mai inganci da cigaba mai ɗorewa.

Wannan na zuwa ne biyo bayan rahoton da Sashen Lura da Tattalin Arziki da Zamantakewa na MƊD ya fitar ranar Talata, inda ya ce yanzu yawan al’ummar duniya ya kai mutum biliyan takwas.

Shugaban NPC, Malam Nasir lsa Kwarra ya ce, yawan al’umma da Nijeriya ke da shi kadara ce ga ƙasa wadda za a yi amfani da ita wajen samar da ci gaba mai ɗorewa.

Ya ce, ba da daɗewa ba Nijeriya ta ƙaddamar da wata sabuwar doka ta ‘National Policy on Population for
Sustainable Development (NPPSD)’, dokar da ya ce ba ta da wata manufa wuce inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.

Don haka ya yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da sarakuna da shugabannin addini, hukumomi da sauransu, da a bai wa dokar haɗin kai don cimma manufarta.

Rahoton na MƊD ya nuna cewa, a halin da ake ciki ƙasar Indiya za ta ɗara China yawan al’umma ya zuwa shera ta 2023.