Ɗan Majalisa ya yanke jiki ya faɗi ana tsaka da yaƙin neman zaɓen Tinubu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Legas mai wakiltar mazaɓar Mushin II, Sobur Olayiwola Olawale ya rasu.

Olawale wanda aka fi sani da Omititi, na cikin ’yan siyasar da suka halarci taron ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen dan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu a Jos, babban birnin Jihar Filato.

Rahotanni sun bayyana cewa, marigayin ya yanke jiki ya faɗi a wajen taron kuma daga bisani ya ce ga garinku nan.