Nijeriya ta zama ta shida a jerin ƙasashe mafi yawan al’umma – MƊD

*Yayin da yawan al’ummar duniya ya kai biliyan takwas

Daga BASHIR ISAH

A halin da ake ciki, Nijeriya ta zama ƙasa ta shida daga jerin ƙasashe mafi yawan al’umma a faɗin duniya.

Wannan ya biyo bayan hasashen da Sashen Lura da Sha’anin Tattalin Arziki da Zamantakewa na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi kan cewa, yawan al’ummar ƙasar ya kai miliyan 216.

MƊD ta bayyana hakan ne ranar Talata albarkacin bikin Ranar Yawan Alumma ta Duniya na bana.

A cewar MƊD kawo yanzu, a ƙiyasce yawan al’ummar duniya ya kai mutum biliyan takwas.

Rahoton Majalisar ya nuna hasashen da aka yi ya taƙaita ne kan wasu ƙasashe guda takwas da suka haɗa da: Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo, Masar, Habasha, Indiya, Nijeriya, Pakistan, Philippines da kuma Jamhuriyar Tanzaniya.

Kazalika, rahoton ya ce ƙasar Indiya za ta ɗara China yawan al’umma ya zuwa baɗi idan Allah Ya kai mu.