Xi Jinping: Sin na goyon bayan shigar da Ƙungiyar AU G20

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Da safiyar yau Talata ne aka buɗe zaman farko na taron kolin G20, a tsibirin Bali na ƙasar Indonesiya, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya halarci taron, ya kuma gabatar da jawabi.

A jawabin nasa Xi Jinping ya ce, a halin yanzu, ana fuskantar babban ƙalubalen raya ƙasashen duniya.

Don haka ya kamata mambobin G20 su sauke nauyin dake bisa wuyansu a matsayinsu na manyan ƙasashen duniya, domin neman bunƙasuwar ƙasa da ƙasa, da tallafawa alummun duniya, yayin da ake tabbatar da ci gaban duniya baki ɗaya.

Ya kuma ƙara da cewa, a halin yanzu, ƙasashen duniya, musamman ma ƙasashe masu tasowa suna fuskantar ƙalubalen raguwar tattalin arziki.

Don haka ya ba da shawarar kafa dangantakar abokantaka ta neman farfaɗo da tattalin arzikin duniya, da mai da aikin neman ci gaba, da raya alumma a matsayin babban aikin da aka sanya gaba, tare da mai da hankali kan buƙatun ƙasashe maso tasowa.

Kazalika ya ce ƙasar Sin tana goyon bayan shigar da ƙungiyar tarayyar ƙasashen Afirka wato AU ƙungiyar G20.

Haka kuma, cikin jawabinsa, shugaba Xi ya bayyana cewa, a halin yanzu, ya kamata a nemi ci gaban da kowace ƙasa za ta iya cin gajiya.

Ci gaban da kowace ƙasa za ta ci gajiya tare, haƙiƙanin ci gaba ne da ake buƙata.

Ya kamata ƙasashen dake kan gaba wajen samun ci gaba, su ba da taimako yadda ya kamata ga sauran ƙasashe, da kuma samar musu ƙarin damammakin da suke buƙata.

Ya ce, ƙalubaloli masu tsanani da ake fuskanta wajen neman bunƙasuwar ƙasashen duniya, su ne babu isashen hatsi da makamashi.

Kuma, muhimmiyar hanyar da za mu yi amfani da ita wajen shawo kan waɗannan ƙalubaloli ita ce, yin haɗin gwiwa kan aikin sa ido a kasuwanni, da kuma kafa manyan kasuwannin buɗe ƙofa ga waje, domin ƙarfafa tsarin samar da kayayyaki cikin haɗin gwiwa, da kuma daidaita farashin kayayyaki yadda ya kamata.

Bugu da ƙari, Xi Jinping ya ce, a yayin babban taron wakilan Jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin karo na 20 da aka yi watan jiya, an tabbatar da burin ci gaban kasar Sin da na JKS cikin shekaru 5 masu zuwa.

Kuma ƙasar Sin za ta tsaya tsayin daka wajen neman bunƙasuwarsu cikin lumana, da zurfafa aikin kwaskwarima, da kuma ƙara buɗe kofa ga waje, domin neman farfaɗowar ƙasar Sin baki ɗaya ta hanyar zamanintar da ƙasar.

Mai Fassarawa: Maryam Yang

By Editor