Finidi George ya bayyana dalilan ajiye muƙamin mai horar da Super Eagles.
Tsohon dan wasan Ƙungiyar kwallon kafa ta Ajax ya bayyana haka ne a wata takardar ajiye aiki da ya aikewa shugaban hukumar kwallon ƙafa ta Najeriya Alhaji shehu Gusau.
Hakan ya biyo bayan canjin da ake so ayi wa tawagar masu aiki da mai horar wa.
“Ina miƙa saƙon godiya da hukumar ƙwallon kafa ta Najeriya da ita kanta Ma’aikatar wasannin ta ƙasa”
