Daga USMAN KAROFI
A yau Lahadi ne Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ya samu nasarar jagorantar idin Babbar Sallah a Birnin Kano.
Gabanin zuwan ranar sallar, an samu barazanar tsaro a Jihar Kano, inda Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta haramta hawan sallah a faɗin jihar biyo bayan taƙaddamar da ke wakana kan karagar Masarautar Kano.
A kwanakin baya ne Gwamnatin Jihar Kano ta rattaɓa hannu kan dokar da ta rushe masarautun jihar guda biyar kuma ta dawo da tsohuwar dokar Masarautar Kano ta asali, wanda hakan ya share fagen dawo da Sarki Sanusi a matsayin Sarkin Kano.
Wannan lamari ya kai ga runtuma zuwa kotuna, waɗanda suka bayar umarni masu karo da juna, inda aka samu shakkun wa ke da ikon hawa karagar mulkin Masarautar Kano tsakanin Sarki Sanusi da tuɓaɓɓen Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero.
Wannan ne ya sa yayin da sallah ta ƙarato aka shiga fargabar wanda zai jagoranci idi a jihar tsakanin sarakunan da ke jayayya da juna.
A cikin waɗanda suka halarci sallar idin da Sarki Sanusi ya jagoranta, akwai Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da sauran jiga-jigan gwamnatin jihar.
Bugu da ƙari, bayanai sun shaida wa Blueprint Manhaja cewa, Gwamna Abba zai kai ziyarar Hawan Daushe, kamar yadda gwamna ya saba yi duk lokacin bukukuwan sallah a Gidan Sarkin Kano da ke Ƙofar Kudu. Sai dai ba a tabbatar ko Sarki Sanusi zai hau doki ya yi kewayen gari, kamar yadda al’adar hawan ta tanada ba.
Haka nan kuma a na sa ran sarkin zai je Hawan Nasarawa a Fadar Gwamnatin Jihar Kano ranar Talata, amma a mota, maimakkn dawakai yadda aka saba.
