Dan Ministan Ayyuka, David Umahi ya zama Shugaban ƙaramar Hukuma a Ebonyi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Dan Ministan Ayyuka na Tarayya kuma tsohon Gwamnan Jihar Ebonyi, Sanata David Umahi, mai suna Osborn Nweze Umahi, an rantsar da shi a matsayin Shugaban ƙaramar Hukumar Ohaozara da ke Jihar Ebonyi.

Osborn Umahi mai shekara 28 ya yi rantsuwar kama aiki ne a ranar Talata, bayan nasarar da ya samu a zaɓen ƙananan hukumomin Jihar Ebonyi da aka gudanar ranar 22 ga Agusta, 2026, inda ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ne ya rantsar da sabon shugaban ƙaramar hukumar, a wani biki da ya samu halartar manyan ’yan siyasa da jami’an gwamnati, ciki har da mahaifinsa, Ministan Ayyuka, Daɓid Umahi.

Da rantsuwarsa, Osborn ya fara gudanar da aikinsa a hukumance a matsayin Shugaban ƙaramar Hukumar Ohaozara.

A lokacin yaƙin neman zaɓensa, sabon shugaban ƙaramar hukumar ya yi alƙawarin mayar da hankali kan inganta ayyukan more rayuwa, ƙarfafa gwiwar matasa, tallafa wa harkokin kasuwanci da kuma inganta samar da muhimman ayyukan gwamnati ga al’ummar ƙaramar hukumar.

Haka kuma, Osborn Umahi ya yi alƙawarin cewa zai yi watsi da karɓar albashinsa da sauran alawus-alawus ɗinsa a tsawon lokacin da zai yi yana riƙe da muƙamin, yana mai cewa burinsa na shiga siyasa shi ne yi wa al’umma hidima ba neman wata fa’ida ta kuɗi ba.

Nasarar da ya samu ta zo ne yayin da jam’iyyar APC ta lashe dukkan kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 13 na Jihar Ebonyi a zaɓen da aka gudanar ranar 22 ga Agusta.

Osborn Umahi injiniya ne kuma ɗan kasuwa. Ya karanci aikin injiniyan gine-gine a Jami’ar Surrey da ke ƙasar Ingila, kafin daga bisani ya samu digiri na biyu a fannin Kuɗi da Gudanar da Zuba Jari a Jami’ar Aberdeen da ke Scotland.

Mahaifinsa, Sanata Daɓid Umahi, ya kasance Gwamnan Jihar Ebonyi daga shekarar 2015 zuwa 2023, kafin daga bisani a naɗa shi Ministan Ayyuka na Tarayya.

Yanzu haka sabon shugaban ƙaramar hukumar zai fara aiwatar da alkawuran da ya yi a lokacin yaƙin neman zaɓe, musamman a fannoni na bunƙasa ƙananan hukumomi, ayyukan more rayuwa, ƙarfafa matasa da inganta ayyukan gwamnati ga al’umma.

By ukarofi

Leave a Reply