Dandalin shawara: Ina ɗauke da cutar ƙanjamau da mijina ya mutu ya bar ni da ita, kuma yanzu Ina son aure

ci gaba daga makon jiya

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Assalamu alaikum wa rahmatulla. ‘yar’uwa barka da ranar Juma’a mai albarka. Allah Ya raya zuri’a. Ya ayyuka. Dan Allah sirrina zan faɗa ma ki, duk da na san ba ki bayyana suna. Wallahi Ina ɗauke da cutar Sida. Kuma Allah ne sheda ban same ta ta hanyar banza ba. Mijina a wurin yawace-yawacensa ne ya kwaso ta, ya zo ya sa mun. ban san Ina da ita ba, sai ranar da ya sanar da ni yana tare da cutar, kuma ya shekara biyu da ita. To bayyan na tabbatar ni ma na samu, muka shiga shan magani asiri rufe. Sai dai a shekarar baya ne ya zo ya rasu, na yi fargaba da sauran su yanzu kuma na kwaɗaita da son aure, don Ina da sauran ƙurciyata. Duk yadda zan cire abin na yi, amma kin san sha’ani na sha’awa, ya bar mun dukiya ni da ‘ya’yana wanda ya sa manema ke ta zuwa, sai dai Ina tsoron sanar da su kan matsalata don gudun su qi amincewa kuma su je su fallasa. Ki taimaka mun da shawara yadda zan samu biyyan buƙata ta ba tare da asirina ya tonu ba, kin dai san yadda ake ƙyamar masu ciwon. Na gode, Allah Shi yi albarka.

AMSA:

Shin kuna da masaniyar kyara da ƙyamar da kuke nuna wa masu wannan cuta gudunmuwarku ce ga ita wannan ƙwayar cutar? Yayin da kuka ƙyamace su, za su iya kauce wa waɗannan ababe biyu da na faɗa, za su rage damuwa da cin abinci, wasu da yawa su ƙi karvar magani domin ganin da suke gara mutuwarsu da rayuwar ƙyama da suke ciki, ga kuma uwa uba qara wa ƙwayoyin halitta da ke yaƙi da cutar wani nauyi na ciwon damuwa.

Wannan ne ya sa a Arewa masu mutuwa cikin sauri akan wannan cutar suka fi masu rayuwar walwa da wannan cutar yawa. Kuma kaso mafi yawa sai sun kai matakin AIDS ɗin, hakan zai sa ta bayyana a jikinsu ta hanyar yawan ciwo, ƙuraje, rama da sauran su.

A wani ɓangaren zan ce ba ku yi wa wasu adalci ba a game da wannan cuta, kuma ba ku tausaya wa waɗanda ƙaddara ta kai su ga cutar ba su suka kai kansu ba. Misali, macen da ta kange kanta a gidan miji, ta ji tsoron Allah bata zubar da kanta a wajen wasu mazan ba, sai dai an jarrabe ta da mijin banza dake ƙetarar ‘ya’yan mutane, ya kwaso wannan cuta, ya zo ya kawo wa salihar matarsa (a nan na ke janyo hankalin mata, babu laifi idan kin fahimci mijinki na yawan neman mata ki nemi hanyar kare kanki, ko da kuwa ta dagewa sai ya yi amfani da kariya kafin ya kusance ki, ko ta yawan neman yin gwaji ko ta hanyar magani da har na ji labarin akwai na Hausa, wai na kariya daga kamuwa da cutar, amma ban san gaskiyar zance kansa ba, sai dai kina iya bincikawa. Kuma ko a Musulunci ba ki yi laifi ba, saboda kare kai daga cuta ba laifi ba ne, asalima suna daga cikin dalilan da aka yarje ma ki idan kika samu tabbaci kan su za ki iya neman rabuwa ba tare da haɗuwa da fushin Allah ba) ko mazan da suka ɗauka a aski ko a wurin matansu da ke shashanci ko ta allura da sauran ababen da muka lissafa.

Don haka ku yi mu’amala da masu cutar da kyautatawa, kuma ku fahimci cutar kafin ku yanke hukunci kanta, yin hakan zai iya kawo sauƙi a tare da waɗanda ke ɗauke da ita.

Idan na koma ɓangaren dalilin wannan dogon zance, ‘yar’uwa kin zo da abu mai wahala da kuma sauƙi, wahalar sa irin kallon da ake yi wa cutar da kuma jahiltar ta da aka yi a Ƙasar Hausa, wannan zai sa ba duk namiji a hausawa ne zai iya aurenki da masaniyyar kina tare da wannan cuta ba.

Sauƙin wannan kuwa idan kin haɗu da wayayye da ya san cutar kuma ya fahimce ta, to shi kam ba zai ganki a matsayin abin ƙyama ba, saboda ya riga ya san ba hatsari kike ga tasa lafiyar ba.

Shawara ki sa Allah a gaba, ta hanyar bin umurninsa a irin wannan matsala, wato faɗar gaskiya ga duk wanda ya zo neman aurenki matuƙar kin ƙudere aniyar auren shi. Sai dai hanzari ba gudu ba, a wannan zamani da muke ciki, maza da yawa zuciyarsu ta mutu, kwaɗayi ya yi katutu a zukatan su, komai za su yi idan dai akan kuɗi ne.

Kwanaki na ci karo da wani rubutu a kafafen sada zumunta na wani da ya auri wata mai irin wannan lalurar da sunan shi ma yana ɗauke da ita, bisa ga ƙarya don kawai hango wa kansa da yake tana da abinda zai tatse na daga dukiya, shekara ɗaya tana tare da shi bai tava ta da suna auratayya ba, bisa hujjar ƙarya na ba shi da lafiya.

To kinga akwai buƙatar ki yi taka-tsan-tsan da wanda kika zaɓa koda kuwa ya amince da cutar, ki tabbatar kin shimfiɗa wasu sharuɗa da za su iya ganar da ke idan ƙudurinsa kawai dukiyarki ce.

Ba wai na ce auren don dukiya ya haramta ba ne, sai dai irin yadda mutanenmu ke yi ne keda cutarwa, idan ya aure ki don kuɗi, da yawa fa ba fatansu ku ci tare ba, burinsu duk abinda kike da shi ya dawo hannunsu, don haka kina ba su suna ƙara neman ƙari, kuma da za ki biye masu akwai yiwar ko dukiyar dukka kika ba su ba zai sa su zauna da ke lafiya ba, saboda ba ke suke so ba, sai su ci moriyar ganga kawai, hakan na nufin rabuwa ko rayuwar wulaƙantawa.

Za mu kawo ƙarshen wannan tambayar a sati mai zuwa.