2023: Kotu ta umarci INEC ta ci gaba da yi wa ‘yan ƙasa rijistar Katin Zaɓe

Daga WAKILINMU

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta Abuja ta bai wa Hukumar Zabe Mai Zama Kanta ta ƙasa (INEC) umarni kan gaggauta komawa ta ci gaba da yi wa masu zaɓe rijistar zaɓen 2023.

Kotun ta buƙaci INEC ci gaba da shirin nata har sai ya rage kwana 90 kafin zaɓen na 2023.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a Inyang Ekwo, ya bai wa INEC umarnin ta tabbatar ba ta hana dukkan ’yan Najeriya da shekarunsu ya kai 18 damar yin rajistar ba.

Hukuncin da ya yanke ranar Talata, Alƙalin ya ce haƙƙi ne a kan INEC ta tabbatar da ta yi shirye-shiryen da suka kamata daidai da doka wajen gudanar da shirin.

Ekwo ya ce, “Ƙarar ta samu nasarar ne saboda cancanta.”

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), ya rawaito cewa Anajat Salmat da wasu mutum uku ne suka shigar da ƙara mai lamba: FHC/ABJ/CS/1343/2022 a kan INEC inda suka nemi a ci gaba da shirin yi  wa jama’a rijistar zaɓe.

Sun buƙaci hakan ne domin bai wa ’yan ƙasa da ba su samu yin rijista a baya ba damar yin haka, kasancewar da sauran lokaci kafin babban zaɓen 2023.