Dandalin shawara: Mijina ya nisanta kansa da zama uban cikin da ke jikina

Spread the love

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga AISHA ASAS 

TAMBAYA: Aisha Asas barkanki da yau. Ya jama’a dai. To madalla. Don Allah ki taimaka min yadda ki ka saba ba wa mutane shawara da suke amfana da ita har ta yi masu aiki ga abinda yake ta damun rayuwarsu. 

Kina ji na ko, wato miji ne nake tare da shi da ban san kowanne irin mutum ne ba, ya sani duk daren Allah sai ya………..(mun cire kalmomin saboda rashin dacewar ta). Kuma kar ki ce sau ɗaya, har ba iyaka. To wai yanzu na yi ciki, asibiti an ce Ina ɗauke da juna biyu na wata biyar, amma mijin nawa ya ce shi bai san zancen ba, wai wallahi ba cikin sa ba ne. Sai faɗa yake yi wai tun kan ya aure ni ma Ina ba shi yana……………, don haka ya san ko da can ba shi kaɗai ba ne bare yanzu. Shi lallai ba zai amshi cikin ba. 

Ki ba ni shawara yadda zan ƙwaci ‘yancina kan wannan tozarci da mijina ke shirin yi min don Allah. Na gode sosai da sosai.

AMSA: Menene hukuncin da addini ya shirya kan irin wannan matsala taki?

Kamar yadda muka sani babu wata matsala ko rikici da zai samu mutum face addinin Musulunci ya bayyana mafita kansa tun gabanin ya same shi, sai dai rashin ilimi wani lokacin ke sa mu shiga ruɗani da rashin sanin inda za mu dosa da matsalolin mu.

Kafin mu faɗi matakai da hukuncin da aka tanada dan warware wannan matsala, zan soma ne da tambayar ko kin san hukuncin zargi a aure?

Aya ta 21 a cikin suratul Rum ta littafi mai tsarki, Allah maɗaukakin sarki ya ce, “kuma akwai daga ayoyinSa, Ya halatta maku matan aure daga kanku, domin ku samu natsuwa daga gare ta, kuma Ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku…..”

Idan muka ɗauki wannan ayar, za mu fahimci shi aure ba ana yin sa ba ne kawai don kwanciyar aure, ana yin sa don samun natsuwa, natsuwar nan ta haɗa da yarda. Duk inda aka ce miji na zargin matarsa ta aure, to fa ba shi da natsuwa, domin a duk inda yake yana tunanin tana can tana wani abin rashin ɗa’a.

Malamai mafi rinjaye sun tabbatar da cewa, idan zargi ya yawaita a tsakanin ma’aurata, to auren karan kansa babu shi, wasu na ganin sai sun furta sakin, yayin da wasu ke ganin idan har zargin ya kai zargi shi kansa sakin ne.

Abin nufi a nan dai shi ne, mijin da ya kasa samun natsuwa da matarsa, a duk lokacin da ya ba ta baya zuciyarshi na saƙa mashi tana aikata ɓarna, to babu auren. Kinga kuwa tun kafin ki samu cikin ma auren naku yake da rauni.

Zance na biyu wanda akansa ne muke magana, wato hukuncin da ya kamata ki ɗauka ko abinda ya kamata ku yi kan matsalar.

Akwai abinda ake kira da ‘Li’ani’, a luggance kalmar na nufin la’ana, a shar’ance kuwa wani hukunci ne da Musulunci ya tanada don warware iren wannan matsala. Wato rantsuwa ta la’ana don barrantar da kai daga abinda abokin zama ya jefe ka da shi, ko akan abinda ka ke zargin abokin zaman ka da shi.

Idan aka wayi gari an samu matsala tsakanin ma’aurata da ta kai ga miji ya musanta ciki ko ɗan da matarsa take da shi, to idan sun je kotu, kowanne daga cikin su ya tsaya kan maganar sa, wato shi ya ce ba cikin sa ba, ita kuma ta ce cikin sa ne, to kowanne zai yi rantsuwa. Misali mijin zai ce, ya rantse cikin jikin matar shi ko ɗan da matar ta haifa ba na shi ba ne, idan na shi ne Allah Ya yi masa kaza da kaza. Ita ma ta yi rantsuwa nashi ne, idan ƙarya take yi Allah Ya yi mata kaza da kaza. Wannan shi ake cewa la’anar, wato saboda munin abin.

Idan suka yi hakan kuwa, malamai sun ce, auren ya ƙare a take, kuma haƙƙin ɗan yana wurin matar har sai abinda ya bayyana da ya canza lafazin su. Wannan kenan, sai dai kamar yadda na ce a baya, zamani ya zo da sauƙi, inda za ku iya warware wannan matsala tun kan ta kai ku ga zuwa kotu.

Shawara ki sanar da shi don ga dukkan alama dukkanku ba ku san da cewa za a iya sanar da ku a asibiti cikin ko na wa ye ba. Idan ku ka je wurin likita, ku ka yi masa bayani, shi zai sanar da ku yadda za a yi. Idan kuwa za ku iya jira har a haifi cikin, nan ma za a iya samar maku da amsa bayan ɗan ya zo duniya.

Abu na ƙarshe, idan har ababen da ki ka faɗa haka ne, to auren kansa naku na da matsala da tabbas ya kamata ku nemi malami don sanin yadda za ku yi, domin zai iya yiwa ku koma yin zaman zina da sunan aure. Ki samu malami, ki masa bayanin da ki ka yi min, idan zai yiwu ke da mijin ku same shi, hakan zai taimaka ƙwarai da gaske, domin shi zai san idan sha’anin mai gyaruwa ne, sai ku gyara kura-kuran ku, idan kuma rabuwar ce, sai kowa hankalinsa ya kwanta.

Lallai masu tsayuwa akan iyakokin Allah su ne masu rayuwa mai daɗi.

By ukarofi