Daga AISHA ASAS
Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin kwalliya na jarida mai farin jini Manhaja, sannunku da jimirin bibiyarmu.
Kasancewar sanyi ya fara kunno kai, za mu fara karkata a ɓangaren ababen da ke taimakon fata don fuskantar wannan lokaci cikin sauƙi. Kamar yadda kuka sani, shafin Kwalliya na tafiya daidai da lokaci ne don amfanin masu karatu.
Kafin komai bari mu fara da bayanan masana kan irin abinda yake cikin man kaɗanya na daga sinadarai.
Masana sun tabbatar da samuwar fatty acids a cikin man kaɗanya, wato wani sinadari da ke gina fata. Samuwar waɗanan fatty acids ɗin a man kaɗanya ne ke ba wa man damar shigar da damshi cikin fata wanda ke hanata bushewa a lokuta irin na sanyi.
Da wannan ne za mu iya cewa, amfani da man kaɗanya a lokacin sanyi na da matuƙar muhimmanci ga fata, domin yana tsirar da fata daga bushewa.
Akwai oleic acid (kashi 40 zuwa 60 bisa ɗari) a cikin man kaɗanya, kuma aikin wannan sinadarin shi ne sanya fata ta zama mai laushi. Wannan na nufin amfani da man kaɗanya na sa laushin fata.
Sannan kuma masana sun tabbatar da samuwar stearic acid (kaso 20 zuwa 50 bisa ɗari) a ciki, wanda shi yana ba wa fata kariya ne, kuma ya hana ta saurin bushewa.
Linoleic acid ( kaso 3 zuwa 11 bisa ɗari) na ɗaya daga cikin ababen da masana suka ce ana samu a cikin man kaɗanya, shi kuma aikinsa taimako ne wurin gyaran fata, musamman ma ga masu busashiyar fata (dry skin) ko mai yawan kumburi.
Baya ga waɗannan, akwai palmitic acid ( kashi 2 zuwa 9 bisa ɗari), wanda kuwa kariya ce ga fata, yana hana ta lalacewa ko in ce samun matsala.
Ko a iya nan muka tsaya zai iya gamsar da mai karatu cewa, man kaɗanya babban jarumi ne da ya zama kariya ga fata a kowane lokaci, bare kuma lokacin sanyi, wanda fata ta fi shiga hatsarin bushewa da kuma tsagewa.
Saidai darasin namu ba zai tsaya a iya nan ba, domin za mu faɗaɗa har mu fayyace duk wani albarka da ke cikin man na kaɗanya, wanda zai taimaka matuƙa wurin sanin muhimmancin sa da kuma hanyoyin amfani da shi.
Idan mun fahimci wannan, mu je ga irin nau’in bitamin da ke cikinsa.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa.
