
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Laraba tawagar Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro, Malam Nuhu Ribaɗu, ta gana da Ɗan Majalisar Amurka, Riley Moore a Birnin Washington DC domin warware matsalolin zarge-zargen tauye ƴancin addini da ta’addanci a Nijeriya, lamarin da ya tayar da hazo a ƴan makonnin da suka gabata musamman a fagen siyasar Amurka.
Ɗan majalisar, wanda ɗaya ne daga cikin waɗanda Shugaba Donald Trump ya umarta su bincike zargin kisan kiyashi ga Kiristoci a Nijeriya, ya bayyana zaman tattaunawar a matsayin ‘amana da ci-gaba’ game da al’amarin.
Ya ce, zaman ya ta’allaƙa ne akan rikicin addini, ayyukan daƙile ta’addanci, agajin tsaro da bada kariya ga yankuna marasa galihu a sassan ƙasar.
Tawagar Nijeriyar ta ƙunshi manyan jami’an tsaro da difulomasiyya waɗanda suka haɗa da Ƙaramar Ministar Harkokin Waje, Bianca Ojukwu; Sufeto Janar na Ƴan sanda, Kayode Egbetokun; Antoni Janar na Ƙasa, Lateef Fagbemi, SAN; Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Olatunbosun Oluyede; da kuma Shugaban Sashen Leƙen Asirin Sojoji, Laftanal Janar E.A.P Undiendeye.
Haka kuma, akwai manyan jami’ai daga ofishin NSA da na ofishin hidimar difulomasiyyar Nijeriya a Amurka.
A wani rubutu da Moore ya wallafa ta kafar X, ya bayyana cewa an yi amfani da zaman ne wajen isar da saƙon haƙiƙanin al’amarin inda Amurka ta tsammaci Nijeriya ta ɗauki matakai masu ƙarfi wajen kawo ƙarshen ta’addancin da ake yi wa Kiristoci a ƙasar.
Ya kuma jaddada cewa Amurka a shirye take ta tallafa wa Nijeriya a ƙoƙarinta na daƙile ayyukan ta’addancin Boko Haram, ISWAP da sauran ƙungiyoyin ta’addanci a ƙasar musamman waɗanda ke ayyukansu a Arewa maso Gabas da yankin jihohin tsakiya, wato Middle Belt.
Hakan na zuwa ne ƙasa da wata guda da Shugaba Trump ya ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa akanta (CPC), wanda hukunci ne da ake laƙƙana wa ƙasashen da ke tauye ƴancin addini.
