Dandalin shawara: Shekara tara da aure, mijina bai taɓa kusanta ta ta sananniyar hanya ba

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Don Allah ki taimaka min da shawara. Ni dai daga ƙauyen……..na aiko da wannan saƙo. Ina da shekara 13 aka yi min aure, kuma ni ban san komai da ake yi da namiji ba. Da ya zo kusanta ta ta farko sai ya yi ta baya. Ban gane ba don na ɗauka haka ake yi. Haka ya yi ta yi har muka yi shekara shida, uwaye na ta ƙorafin ban haihuwa. To sai ya zamana na fara samun matsala a ta kashi na, idan tusa ta zo min nai ƙoƙarin hana ta fita sai na kasa, kuma Ina yin ƙoƙarin matse ta. Da abin ya dinga sani kunya sai na gaya ma shi, sai ya ce, ai basir ne zai samar min magani. Bayan wasu shekaru kamar uku zuwa huɗu sai kuma na ƙara samun wata matsala. Idan Ina ciwon ciki, Ina gudawa, sai in ta yin sa a jikina, saboda ina kasa riqe shi idan ya taso. Ranar dai sai na fara tunanin ko dai wani ciwo ke tare da ni. Ba na mu’amala da mutane sosai don ba ya so, don haka ba ni da ƙawaye, sai dai muna hulxar mutunci da wata maƙwabciyarmu ta yamma da mu mai suna…. don ita kan shigo idan ba ya nan. Ranar dai da batun zuci ya yi min yawa, sai na tambaye ta ko ita tana fama da irin matsalar da nake da ita, sai ta ce a’a. A nan ta ce na hanzarta zuwa asibiti don kar ya zame min irin matsalar masu kwana da maza ‘yan’uwansu. To abin sai ya sha mun kai, tsayin kwanaki Ina tunanin abinda ya haɗa ni da waɗannan mutane. Bayan kwanaki na kasa samun sukuni, sai rannan na tambaye ta wai ta ina ake kusantar mace. Ta yi dariya ta shiririce maganar har bayan kwanaki na sake tambayar ta, da taga da gaske ne, shine ta min bayyani wanda ya saɓa wa inda yake min. Ban ɓoye mata komai ba na gaya mata. Ita ta taimaka min na saci jiki bayan ya fita muka tafi asibiti don ba ya barina zuwa asibiti. Nan ne fa likita ta min qarin bayani. Da na yi masa bayani ya hau ni da faɗa, har da barazana. To ita wannan makwabciyata ce ta ce na neme ki a Fesbok tunda wayata tana yi, ita ma ta yi yadda ake yin magana da mutane don ban tava yi ba. Ta gaya min za ki ba ni shawara don ita ma tana turowa. (Allah Ya sa na samo rubutun yadda ya kamata, kasancewar rubutun da aka turo ya ɗan yi wuyar karantawa).

AMSA:

Wannan neman shawara sai ya tuna min da wasu shekaru da suka shuɗe, a lokacin muna makarantar Islamiyya a matakin iftidaiyya. A wani lokaci malamai suka yanke shawarar sanya ilimin jima’i a cikin darussan da za su dinga koya wa ɗalibai. Don haka sai aka ba wa kowane ɗalibi takarda ya kai wa iyayenshi ta neman izini ko ince ta sanar da su ƙudirin su. Abin mamaki kaso mafi rinjaye na iyaye sun aiko ko sun zo da ƙorafin rashin dacewar hakan, a taƙaice dai ba su amince da a koyar da ‘ya’yansu wannan darasi ba.

Abinda suka kasa sanar da kansu shi ne, idan ba su bari an koyar da ‘ya’yansu ta kyakyawar hanya ba, suna da hurumin hana su koya ta mummunar hanya. Sau da yawa iyaye na kuskure ta ɓangaren abinda ya shafi sanin kwanciya, akwai iyayen da ma ke cire yaransu daga islamiyyar da malamai ke masu darasin da ya shafi kwanciyar aure, kuma su ba koyar da yaran za su yi ba. Kuma ba su yi tunanin za su iya samun wannan ilimin ta kafafen sadarwa wadda su da kansu ne za su samar masu da ita.

Tambaya a nan, da malami da yake faɗa daga cikin abinda Allah da manzonSa suka faɗa, da kuma ashararu da ke biye wa ruɗin duniya da kwaikwayo da waɗanda ba su yarda da Musulunci ba, wane ne za ka so ɗanka ya koyi wannnan lamari a wurin sa.

Malami ne zai koya wa ‘yarki sahihiyyar hanyar da za a kusance ta, tare da tsoratar da ita kan hanyar da ta haramta, hakan zai bata damar ganewa idan mijinta ya kuskure. Shi kuma wanda zata koya ko ta labaran batsa ko finafinansu, za su nuna mata duk ɗaya ne matuƙar tana da buƙatar yin hakan.

A wurin malami ne zata san lokacin da bai kamata a kusanceta ba (lokacin jini) da kuma yadda zata tsarkake kanta bayan saduwa. Duk wannan haƙƙi ne da ya rataya kanku iyaye, amma da yawa ba sa sanar da ‘ya’yansu kafin aure, musamman ma iyaye mata. Za ka tarar kaso ɗaya ne bisa ɗari na iyaye mata musamman a Arewacin Nijeriya ne suke zaunar da ‘ya’yansu mata, su fere musu biri har wutsiya kan lamarin mu’amala ta auratayya, sai ku bar su, su je can su ƙarata, ko su mazan su koyar da su. To ta irin wannan damar ne idan sun haɗu da maza masu son zuciya suke nuna masu irin hanyar da suka fi so a matsayin daidai.

Don haka wannan na ɗaya daga cikin gyara da ya kamata iyaye musamman iyaye mata su yi, ku sanar da ‘ya’yanku abin da yake ɓoye na daga mu’amala ta auratayya, ta hakan ne za ku kare su daga son rai irin na wannan bawan Allah, sannan su iya bambance halas da haram a tarayyar.

Idan mun koma kan hukuncin wannan ɗabi’a a Musulunci, hukuncin kusantar mace ta bayanta daidai ne da irin hukuncin kusantar mace a lokacin da ta ke jini, kamar yadda muka taɓa faɗa a wata tambayar, wato haramun.

Sai dai wasu malamai sun bayyana wannan ɗabi’a a matsayin mafi laifi fiye da kusanta a lokacin da mace ta ke al’ada, kamar yadda Imam Ghazzali (R.A) ya rubuta a cikin littafinsa ‘Ihya’ cewa yin jima’i da mace ta dubura ya fi laifi akan yin jima’i da ita yayin da ta ke haila. Sai dai hakan ba yana nufin shi ma kusanta a lokacin haila ba laifi ne babba ba, wannan dai ya ɗara shi a girma.

Annabin rahama ya yi hani kan wannan ɗabi’a a hadisai masu dama, wanda daga cikin su akwai wanda ya sanar da irin matsayin masu wannan laifi a gaban Allah, inda ya ce, “mutumin da ke jima’i da matarsa ta dubura Allah Madaukakin Sarki ba zai dube shi da tausayi ba a ranar tashin ƙiyama.”

Za mu ci gaba.