Jaruma Mercy Aigbe ta musulunta

Daga WAKILINMU

Fitacciyar jaruma a masana’antar fina-finai ta Nollywood, Mercy Aigbe, ta bayyana sunanta na Musulunci biyo bayan musuluntar da ta yi.

Ta bayyana sunan ne a wajen taron lacca na Ramadan da addu’a ta musamman da suka shirya ita da mijinta, Kazeem Adeoti.

Hakan na ƙunshe ne cikin wani faifan bidiyon tattaunawar da aka yi da ita wanda aka yaɗa a kafar sada zumunta na zamani.

An jiyo ta tana cewa, “Insha Allah, sabon sunana shi ne Hajiya Meenah Mercy Adeoti. Meenah mai ɗauke da harafin H.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *