Dangote ya soki ƙarin kuɗin ruwa da CBN ta yi

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya soki sabon ƙarin kuɗin ruwa zuwa kusan kashi 30 cikin 100 da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi.

Aliko Dangote ya ce, yin hakan zai ƙara durƙusa sana’o’i tare da rufe ƙofa ga waɗanda suke ƙoƙarin fara sana’a.

Yayin da yake jawabi a wajen buɗe taron kwanaki uku da ƙungiyar masana’antu ta Nijeriya (MAN) ta shirya a ɗakin taro na Banƙuet da ke fadar gwamnatin tarayya Abuja, a ranar Talata, Dangote ya ce ‘yan kasuwa ba za su iya jurewa halin da ake ciki yanzu ba.

Alhaji Aliko Dangote ya ce, ƙarin kuɗin ruwa ga masu karɓar rance zai hana ‘yan kasuwa da dama zama da ƙafafunsu.

Dangote ya ƙara da cewa, ba lallai a iya samar da sana’o’i da matasa ba matuƙar kuɗin ruwa ya ƙaru sosai.

Har ila yau, attajirin ya ce, hatta kamfanoni ba za su tsira daga shiga cikin matsalar durƙushewa ba idan aka samu ƙarin kuɗin ruwa ya yi yawa.

A watan Mayu, bayan wani taron kwanaki biyu, kwamitin tsare-tsare na kuɗi na CBN (MPC) ya amince da ƙara yawan ƙa’idojin kudi (MPR) a karo na uku daga kashi 24.75 zuwa kashi 26.25 cikin dari.

“Kwamitin tsare-tsare na kuɗi (MPC) na Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya gudanar da taronsa na 295 a ranakun 20 da 21 ga watan Mayun 2024 don duba cigaban tattalin arziki da na kudi da kuma tantance kasadar da ke tattare da hangen nesa.

“Shawarwari na MPC. Hukunce-hukuncen kwamitin sune kamar haka: 1. A daga darajar MPR da maki 150 zuwa kashi 26.25 daga kashi 24.75 cikin 100,” inji Gwamnan CBN, Yemi Cardoso wanda kuma shi ne shugaban MPC.

A ɗaya ɓangaren kuma, Aliko Dangote, ya gano hanyoyin da za a bi don ɗorewar saka hannun jari na cikin gida da na waje tare da jawo sabbin masu zuba jari a cikin ƙasar.

Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka ya ce, don riƙe masu zuba jari daga barin ƙasar da yawa tare da jawo sabbi, dole ne Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da manufofin masana’antu da ke ba masu zuba jarin tallafi da kariya.

A cewarsa, irin waɗannan tsare-tsare sune mafi girman abin ƙarfafa gwiwa ga duk masu zuba jari, masana’antun, na gida da waje.

Masanin masana’antar ya kuma bayyana cewa masu zuba jari na ƙasashen waje, masana’antun za su jawo hankalin kawai idan sun ga cewa masu zuba jari na cikin gida suna da inganci.

A cewarsa, abinda ke jan hankalin ƙasashen waje ba shi ne lokacin da shugaban ƙasa ko wasu hukumomin gwamnati suka fita aasar waje neman jarin waje ba.

“Ina bada shawarar cewa manufofin gwamnati su tallafa, su kare masana’antun da ake da su domin wasu su san cewa jarin su ma za a kare.

“Shin akwai wani abin ƙarfafawa fiye da wannan? Ba na tunanin haka. Saboda haka, cikin tawali’u na ƙaddamar da cewa manufar masana’antu da ke tabbatar da masu zuba jari na tallafi da kariya ita ce mafi girman abin ƙarfafawa ga dukan masu zuba jari na gida da na waje,” inji shi.

Dangote ya kuma jaddada muhimmancin samar da wutar lantarki mai araha, da kuma samar da kuɗaɗe don cigaba da jawo masu zuba jari da masana’antu.

Ya ce, tsayayyiyar wutar lantarki mai araha da kuma samun damar masana’antu da masu zuba jari za su tabbatar da ci gaba, masana’antu da wadata a Nijeriya.

By ukarofi