Daraktan yaƙin neman zaɓen Obi ya sha kayi a garinsa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Darakta Janar na yaƙin neman zaɓen ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar Labour, Akin Osuntokun, ya faɗi zaɓe a ƙaramar hukumarsa ta haihuwa.

Jam’iyyar APC mai mulki a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu, 2023, ta lashe zaɓen Shugaban Ƙasa da gagarumin rinjaye a Ekiti ta Yamma.

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya doke takwaransa na Jam’iyyar LP Peter Obi, wanda ya zo na uku.

A sakamakon da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, jami’in tattara bayanan ƙananan hukumomi ya bayyana, Jam’iyyar APC ta lashe dukkan gundumomi 11 na ƙaramar hukumar.

Jam’iyyar ta samu ƙuri’u 14,516, LP ta samu ƙuri’u 391, Jam’iyyar PDP ta samu 4,318 sai New Nigerian Peoples Party, NNPP 10.