Dalilin da ya sa kayan zaɓe suka makara a wasu mazaɓun — INEC

Daga AMINA YUSUF ALI

Chief Emmanuel Chike, wani ma’aikacin INEC ya bayyana cewa, rashin soma kasafta kayan aikin zaɓe a kan kari tun a ranar Juma’a shi ne ya yi sanadiyyar samun tsaiko wajen rarraba su ga mazaɓu a ranar zaɓe ranar Asabar.

Chike, jamiin rajista (RAC) a garin Fatakwal Ƙaramar Hukumar Fatakwal ya bayyana wa ‘yan jaridu a ranar asabar cewa, sai ƙarfe 6 na yammacin Juma’a sannan hukumar INEC ta soma kasafta kayan aikin da za a rarraba a mazaɓu.

Haka kuma a cewar sa, wasu jami’an ma sai ranar Asabar ɗin da sassafe wato ranar zaɓen sannan suka fara kasafta kayan aikinsu da za su kai wuraren da za a yi zaɓen.

Wannan a cewarsa shi ya kawo tsaikon kai kayan aikin zuwa wuraren zaɓen, a ranar zaɓen. Kuma wurare da dama ma wannan tsaikon kai kayan zaɓen ya shafe su.

Chike, ya yaba da yadda al’umma suka yi tururuwa wajen fitowa don kaɗa ƙuri’unsu, a cewar sa, wannan alama ce da take nuna cewa mutane sun ƙagu don ganin sun yi amfani da damar da kundin mulki ya ba su wajen zaɓar wanda zai shugabanci ƙasarsu.

Mista Obi Igwe, wani Ejan na PDP ya bayyana cewa, kayan zaɓen sun zo a makare zuwa mazaɓar da yake. Kodayake a cewar sa, ma’aikatan INEC sun ba da haƙuri a bisa tsaikon sannan kuma ya ce zaɓen ya tafi sumul ba tangarɗa.

Mr David Ekwumike, shi ma Ejan na jam’iyyar APC ya je su ba su samu tsaikon zuwan kayan aikin zaɓe ba, kuma an fara zaɓe a kan lokaci sannan ya tafi sumul ba tare da tangarɗa ba.

Haka a jihar Kano wani Malamin jamiar Bayero Kano, Dakta Muhammad Sulaiman Abdullahi da kuma wani ɗan siyasa Mukhtar Mudi Sipikin dukkansu a mazaɓar ƙaramar hukumar Fagge sun nuna rashin jin daɗinsu a kan yadda kayan zaɓen ba su dira a wajensu ba sai ƙarfe 2 na rana. Kuma a wannan lokacin aka fara zaɓen.

Daya daga cikin masu zaɓe a rumfar zave ta 2 a Ƙaramar Hukumar Obiakpor, mai suna Kenwchukwu Udechukwu, ya bayyana cewa, zaɓen ya tafi sumul ba tare da tangarɗa ba ko tashin hankali. A cewar sa, mutane suna bin doka.

A cewar sa ma, zaɓen 2023 ya fi dukkan sauran zaɓuɓɓukan ƙasar nan rashin tangarɗa da rashin hayaniya. Wanna kuma ra’ayin masu zaɓe da dama ne da majiyarmu ta tattauna kuma ta tabbatar da su.