Yadda ɗan takarar gwamnan Bauchi a jam’iyyar APC da matarsa, Ministar Jinƙai suka kaɗa ƙuri’unsu

Daga Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Jihar Bauchi, kuma tsohon shugaban sojin sama, Sadique Abubakar, tare da matarsa, Ministar Harkokin Jinƙai da Cigaban Jama’a, Sadiya Farouk, sun kaɗa ƙuri’unsu a Zirami Ƙofar Fada 001, a Ƙaramar Hukumar Giade a yankin jihar.

Abubakar, a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida ya yaba wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) kan inganta harkokin zaɓe da kuma ɓullo da tsarin tantance masu kaɗa ƙuri’a na BVAS.

Ya ce, “Ya zuwa yanzu, abubuwan sun inganta a yankunan da na ziyarta. Na yi zaɓe a Zirami, Ƙofar Fada Ward kuma an gudanar da komai cikin tsari. Na ga mutane suna jira cikin haƙuri da bin tsari don kaɗa ƙuri’a kuma akwai waɗanda suka kaɗa ƙuri’a kuma na yi farin ciki da aka ba su damar yin aikin da kundin tsarin mulki ya ba su.

“Ina so in yabawa INEC kan yadda suka gudanar da zaɓen a garin Zirami, sun fita kan lokaci kuma ina so in yaba da gagarumin cigaban zaɓen da INEC ta yi.

“Ina kuma so in yaba wa mutanen da suka yi haƙuri har ma a ƙarƙashin rana mai zafi.”

Ita ma uwargidansa Sadiya Farouk ta yabawa jama’ar da suka fito domin kaɗa ƙuri’a musamman mata da matasa.

“Babu wata matsala a tare da na’urar BVAS. A ko da yaushe za a ga mata sun yi yawa, su ne ke kaɗa ƙuri’a. Ban yi mamakin abin da na gani ba kuma saboda sun san haƙƙinsu ne ya sa suka fito su yi amfani da shi,” inji ta.