Ban taɓa ganin zaɓe cikin kwanciyar hankali ba sai a wannan karon – Sanata Barau

Daga RABIU SANUSI a Kano

Ɗan takarar sanata a Kano ta Arewa ƙarƙashin jam’iyyar APC, Hon. Barau I. Jibrin (maliya), ya bayyana cewa bai taɓa ganin zaɓe cikin kwanciyar hankali makamancin wannan ba.

Barau ya bayyana haka ne yayin zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kaɗa kuri’arsa a mazaɓar sa ranar Asabar.

“Ina ganin zan samu lashe wannan zaɓe da tazara mai yawa tsakani na da sauran abokan karawa ta,” in ji Barau.

Kazalika, a yayin gudanar da zaɓen an ji al’umma daga lungu da saƙo wajen gudanar da zaɓen suna kiran sai “Maliyan Kanawa” musamman yadda mutane suka fito da yawa suna kiran sunansa.

Kamar yadda aka sani dai daga yankin Kano ta Arewar an samu da yawan mata sun fito wajen kaɗa ƙuri’ar da yawan su ya kai kimanin kashi sittin cikin 100 da ba a samun hakan ba a tarihin siyasar jihar.

A yankin ta Arewa dai akwai rumfunan zaɓe da yawancin su ba a samu damar fara zaɓen cikin lokaci ba, amma daga bisani malaman zaɓen sun ƙaraso aka kuma ci gaba da sha’anin zaɓe.

Wani abin burgewa a wannan zaɓe shi ne yadda mutane suka kame kansu ba tare da ɗaukar abin da zafi ba, kuma babu tashin hankali sai dai ‘yan matsalolin da ba a rasa ba.